Labaran Bogi da Suka Rika Yawo a Kafafen Sada Zumunta a Makonnin Nan

Labaran Bogi da Suka Rika Yawo a Kafafen Sada Zumunta a Makonnin Nan

  • An yi ta yada labarai da ba su da inganci musamman ganin babban zabe yana karasowa a Najeriya
  • Daga cikin labaran karya da aka ci karo da su kwanan nan akwai zargin shirin yin magudin zabe
  • Ana kuma bude shafukan karya da sunan daukar aiki, ana zargin wannans harrin ‘yan damfara ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Labaran bogi sun yi yawa musamman yanzu da ake sanin yadda duniya ta ke ciki da na’urorin zamani.

Nahiyar Afrika da Najeriya suna cikin inda bayanai da labaran bogi suka bazu a cikin al’umma a lokacin nan da ake ciki.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a kasar waje Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Labaran bogi a 'yan kwanakin nan

Jaridar Legit Hausa takan bibiyi abubuwan da suke faruwa domin ta iya tattaro labaran karya da wadanda ba su tabbata ba.

Daga karshen Satumba zuwa Oktoban 2026, mun samu labaran da kirkirarsu aka yi ko an yaudari jama’a ba a sani ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Labarin yadda Emefiele ya cire biliyoyin kudi daga CBN ya shiga kunnen kotu

Ga wasu kadan daga ciki:

1. Shugaban INEC ya tarbo Bola Tinubu

Wasu sun rika yada hoto da sunan cewa Shugaban hukumar INEC, Jaosh Amupitan ya tarbo Bola Tinubu da ya dawo.

Tinubu ya shafe wata guda yana hutawa a kasar waje. Da ya dawo sai aka ce Farfesa Amumitan ya fito yi masa maraba.

Fact Check Hub ta karyata wannan zance, sun tabbatar da cewa wanda aka alakanta da shugaban INEC, Ibrahim Kabir Masari ne.

Watakila kamanni sun rudi masu yada karyar ne ko kuma ana so ne a bata kimar INEC a idon jama’a gabanin zaben 2027.

2. INEC ta bude shafin rajista

Akwai wadanda suka rika yawo da labarin bogi cewa INEC ta bude shafin rajista - pvc-inecnigeria-org.blogspot.com.

Bincike ya nuna wannan shafi da yake karkashin Blogspot bai da alaka da INEC. Shafinsa shi ne https://inecnigeria.org/.

Wannan ya sa hukumar zaben ta fitar da sanarwa domin karyata batun, ta ce an daina rajistar katin zabe tun a Yulin 2026.

Kara karanta wannan

An yi wa jaruma Fati Muhammad rubdugu kan tallata Tinubu

Wanda ya yi kuskuren ziyartar wancan shafi na bogi zai ci karo da ’yan damfara a Najeriya.

3. Labarin karya na daukar aiki

‘Yan damfara ba su tsaya a nan ba, sun bude shafuka da sunan hukumar NRS mai tattara haraji tana daukar aiki a Najeriya.

Akwai wani shafi da aka bude irin wannan da sunan ‘yan sanda za su dauki sababbin dakaru, labarin da sam bai tabbata ba.

Tun a watan da ya wuce Punch ta rahoto cewa Rundunar ‘yan sanda ta karyata rahotannin da yake ta yawo a dandalin WhatsApp.

Haka zalika jaridar The Sun ta rahoto NRS tana cewa a halin yanzu ba ta daukar aiki a Najeriya.

4. Haduwar Tinubu da shugaban APC a Faransa

A Facebook, wata Blessing Martin tana cikin mutanen da suka rika yada cewa Bola Tinubu ya hadu da shugaban INEC a Faransa.

Labarin da ake yada wa ya ce Bola Tinubu da Nyesom Wike sun hadu Joash Amupitan a kasar wajen domin shirin magudin zabe.

Kara karanta wannan

An fara zuwa kamfen da bindiga, INEC ta yi gargadi kan zubar da jini

Legit Hausa ta yi amfani da shafin https://www.myaifactchecker.org mai tono bayanan karya domin gane sahihancin labarin nan.

Shafin ya karyata ikirarin, kuma kakakin Tinubu, Tunde Rahman ya karyata cewa an gana da farfesan don a murde zabe.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da ziyarci kasar waje kwanaki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Opay da labaran karya a kwanaki

Labaran kanzon kurege sun cika shafukan sada zumunta a kwanakin baya. Rahoton nan ya tattaro karyayyakin da muka ci karo da su.

A lokacin ne a aka rika yada cewa kamfanin Opay zai tafi hutu a Najeriya. Hakan ya sa wasu suka yi ta kwashe kudinsu daga asusun bankin.

An kuma ji jita-jitar cewa jam'iyyar APC ta soke kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima da aka fitar da aka soma kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng