'Zan ba Kowace Mazaba N40m': Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Ɗauki Alƙawari

'Zan ba Kowace Mazaba N40m': Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Ɗauki Alƙawari

  • Dan takarar shugaban ƙasa na YPP ya yi alkawarin bai wa kowace unguwa miliyoyin Naira duk wata idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027
  • Dan takarar ya ce zai samar da jari ga unguwanni 8,809 domin bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi ga matasa
  • Peter Agada ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan yawan karɓar bashi, inda ya yi alƙawarin rage kashe kuɗaɗen ayyukan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar YPP, Peter Agada, ya yi alƙawarin bai wa kowace unguwa Naira miliyan 40 duk wata idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Agada ya ce zai riƙa aika kuɗaɗen ga dukkan unguwanni 8,809 da ke Najeriya domin amfani da su wajen bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Dan takarar shugaban kasa ya ɗauki alkawura
Dan takarar shugaban kasa a YPP, Peter Agada. Hoto: Aaron Auduson.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana tsare-tsarensa idan ya zama shugaban ƙasa.

Dan takarar, wanda masani ne kan gine-gine, ya bayyana cewa manufarsa ita ce tabbatar da kowace unguwa ta dogara da kanta ta fuskar tattalin arziƙi, tare da samar da daidaiton ci gaba a sassan ƙasar.

Agada zai ɗauki ma'aikata 350 a kowace unguwa

Dan takarar ya ce babban aikinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa shi ne ɗaukar ƙwararru domin tsara yadda kowace unguwa za ta bunƙasa.

Ya ce kowace unguwa za ta samu ma'aikata 350 da suka haɗa da masu gine-gine, injiniyoyi, masu tsara birane, ma'aikatan tituna, masu sana'o'i, likitoci da ma'aikatan jinya.

A cewarsa, gwamnatin za ta riƙa tura Naira miliyan 40 ga kowace unguwa duk wata a matsayin jari na farko domin gina tsarin tattalin arziƙin da zai ci gaba da bunƙasa kansa.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da ya fi burge Atiku idan aka taɓa Tinubu yayin amfen

Agada ya ce wannan tsari zai taimaka wajen samar da damar ci gaba ga al'umma tare da rage dogaro da gwamnatin tarayya.

Dan takara ya soki Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da ke neman tazarce a zaɓen 2027. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: UGC

Ya soki Tinubu kan yawan karɓar bashi

Haka kuma, dan takarar ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda gwamnatinsa ke ci gaba da karɓar basussuka domin gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya ce ba ya adawa da karɓar bashi gaba ɗaya, amma yana ganin gwamnatin Tinubu tana karɓar basussuka fiye da kima.

Agada ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen rage kuɗaɗen da ake kashewa a ayyukan gwamnati maimakon ci gaba da karɓar bashi.

Ya kuma yi alƙawarin kafa majalisar kula da harkokin kwangiloli ta ƙasa domin sanya ido kan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Agada ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci a yadda ake tsara kuɗaɗen ayyuka da kuma hana ƙara musu kuɗi fiye da ƙima.

Dan takarar ya kuma yi zargin cewa an ƙara kuɗaɗen wasu ayyukan gwamnatin Tinubu fiye da yadda ya kamata, inda ya kawo aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar a matsayin misali.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya ware gwamnonin Arewa 7, ya ba su shawara kan goyon bayan Tinubu a 2027

Yar takara ta ce maza sun gaza

Mun ji cewa yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar NRM, Esther Okereke, ta ce shugabannin maza da aka yi a tarihi duk sun gaza.

Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su ba mace damar shugabanci a zaben 2027 duba da cewa maza sun kasa kawo sauyi har yau.

Okereke ba tallar jinsinta take yi ba, za ta fi mayar da hankali kan wutar lantarki, tsaro da rikon amana idan ta samu mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.