"Ba Sai An Yi Magudi ba," Gwamna Ya Ce An Kammala Zaben Shugaban Kasa na 2027

"Ba Sai An Yi Magudi ba," Gwamna Ya Ce An Kammala Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya bukatar maguɗin zaɓe domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027
  • Soludo ya kuma kare yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da tattalin arziki da tsaro, tare da yabawa shirinta na tallafa wa ɗalibai
  • Gwamnan ya bayyana cewa lissafi ya nuna cewa an riga an kamma zaben 2027 kuma Tinubu ya samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya bukatar yin maguɗin zaɓe domin samun wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamna Soludo ya ce alamu sun nuna cewa APC ta yi wa yan adawa fintinkau, kuma za ta sake lashe zabe cikin sauki a shekara mai kamawa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin rikici tsakanin Shugaba Tinubu da gwamna a Najeriya

Gwamna Soludo.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo Hoto: Chukwuma Soludo
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa Soludo ya yi wannan hasashe ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani gangamin kamfen ɗin shugaban ƙasa da aka gudanar a dandalin Alex Ekwueme da ke Awka.

Charles Soludo ya ce an gama zaben 2027

“Wannan zaɓe, a iya saninmu, tuni an gama shi ta fuskar nasara da rashin nasara. Shugaban ƙasa ba ya bukatar yin maguɗin zaɓe. Shugaba Tinubu ba ya bukatar yin maguɗin zaɓe,” in ji shi.

Da yake bayyana dalilin ra’ayinsa, gwamnan ya ce tikitin APC na fafatawa ne da jam’iyyun adawa waɗanda ’yan takararsu, a cewarsa, ba su da karfin samun goyon baya a duk faɗin ƙasar.

“Yau a duk faɗin ƙasar nan, a kowace jiha ta Najeriya, maganar Tinubu da Shettima kawia ake yi amma akwai wasu ’yan takara da suke da ƙarfi a wasu sassan ƙasar, sai dai ba su da wani tasiri a sauran sassan.
“Idan ka haɗa komai wuri guda, ka yi lissafi a ranka, za ka ga cewa a zahiri an riga an kammala wannan zaɓe,” in ji Soludo.

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Dalilan da za su ba Tinubu nasara

Ya kuma danganta hasashensa da irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ta yi, yana mai cewa Shugaban ƙasa da mataimakinsa za su yi nasara ne saboda abin da suka gudanar a mulkinsu.

Soludo ya ƙara da cewa APC ta gabatar da tsare-tsaren manufofi da suka fi na abokan hamayyarta ƙarfi, yana mai cewa babu wani ɗan takara da ya fito da sahihin zaɓi na daban gabanin zaɓen.

Gwamna Soludo.
Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo yana jawabi a wurin taro a Awka Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Facebook

Gwamnan ya kuma kare yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa akwai kyakkyawar fahimta a duniya, a ƙasashen waje da kuma cikin gida cewa gwamnatin tana tafiya a kan turba mai kyau.

Ya kawo tallafin da gwamnati ke bai wa ɗalibai ta hannun Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ke amfanar ’yan Najeriya.

APGA ta taya Gwamna Soludo murna

Kun ji cewa jam’iyyar APGA ta taya Gwamna Chukwuma Soludo murnar naɗa shi a kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu.

Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta goyi bayan Tinubu a zaben shugaban ƙasa, yayin da take son ‘yan takararta su lashe kujerun majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262