Obi da Kwankwaso Sun Bayyana Inda Matsala Ta Fito Masu wajen Yakin Neman Zabe

Obi da Kwankwaso Sun Bayyana Inda Matsala Ta Fito Masu wajen Yakin Neman Zabe

  • ‘Yan kungiyar OK sun yarda cewa an fitar da kwamitin yakin neman zaben 2027 ba tare da bin ka’ida ba
  • Wannan ne zargin da jam’iyyar NDC ta yi wa magoya bayan na Rabiu Kwankwaso gabanin a fara kamfe
  • Kakakin OK, Emmanuel Idakwo ya zargi ‘yan APC da kambama sabanin NDC domin bata masu suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tafiyar OK Movement ta magoya bayan Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun yarda an samu matsala a tsarinsu.

OK ta amince cewa ta fitar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba tare da bin duk ka’idojin da suka kamata ba.

Obi/Kwankwaso
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ana kamfe Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ana aiki Peter Obi bai da masaniya a OK

Kakakin tafiyar OK a Najeriya, Emmanuel Idakwo ya shaida haka da aka yi magana da shi a gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Labaran bogi da suka rika yawo a kafafen sada zumunta a makonnin nan

Mista Emmanuel Idakwo ya amsa cewa an fitar da sunayen wadanda su yi aikin yakin neman zabe ba tare da bin ka’ida ba.

“Game da kwamitin neman zabe da aka ce wasu da suke ikirarin ‘yan tafiyar OK ne sun fitar, zan iya fada maka cewa ba a yi abin a hukumance ba.
“Domin ko Peter Obi bai da masaniya game da shi. Kuma ba zai yi wani ‘dan tafiyar OK ya kaddamar da wani abin ba tare da sanin shi ba ba.
“Saboda haka ba a yi shi a hukumance ba. Akwai wata manufa a lamarin.”

- Mista Emmanuel Idakwo

OK ta raba kanta da wasu magoya bayan Obi

‘Yan kungiyar OK suna cikin magoya baya masu zaman kansu da ke tallar Peter Obi da abokin gaminsa, Rabiu Kwankwaso.

Mai magana da yawun OK ya ce akwai alaka mai kyau tsakaninsu da NDC da jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson.

Kara karanta wannan

EFCC: Labarin yadda Emefiele ya cire biliyoyin kudi daga CBN ya shiga kunnen kotu

Premium Times ta rahoto shi yana cewa ba duk abin da aka ga ya fito daga magoya bayan Peter Obi za a alakanta da tafiyar OK ba.

Ana zargin APC da kawo wa NDC matsala

Idakwo ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da yin duk abin da za ta iya domin kawo wa NDC matsala, ta bata mata suna a Najeriya.

Ya dage da cewa kungiyoyin OK, Obidient da Kwankwasiyya duk ba su san da labarin kwamitin yakin zaben 2027 da aka fitar ba.

Ya zargi APC da neman cusa rikici a jam'iyyar NDC ta hanyar zuzuta kananan matsalolin cikin gida.

Idakwo ya ce idan aka duba yanar gizo, ‘yan jam’iyyar APC za a gani suke huro wuta saboda a rika tunani akwai rabuwar kai a NDC.

Peter Obi
'Dan takaran NDC, Peter Obi a garin Sokoto Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

ADC za ta yi aikin malaman zabe a 2027

Kuna da labari cewa jam’iyyar ADC mai hamayya ta ce za ta tattara tare da wallafa sakamakon zaben 2027 daga rumfunan zabe.

‘Yan adawan sun yarda hukumar INEC ce kadai ke da ikon sanar da sakamakon zabe da ayyana wanda ya yi nasara a takara a doka.

Kara karanta wannan

Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC

ADC ta bayyana yadda za ta tabbatar da sahihancin sakamakon da za ta wallafa ko magance bambance-bambancen sakamako ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng