EFCC: Labarin Yadda Emefiele Ya Cire Biliyoyin Kudi daga CBN Ya Shiga Kunnen Kotu

EFCC: Labarin Yadda Emefiele Ya Cire Biliyoyin Kudi daga CBN Ya Shiga Kunnen Kotu

  • Shari’ar Godwin Emefiele da hukumar EFCC tana cigaba da tafiya a babbar kotun tarayya a Abuja
  • Hukumar ta gayyaci wani Darekta a ma’aikatar kudi da ya yi magana kan wasu N124bn da aka cire
  • An dauki kudin lokacin Emefiele yana gwamnan CBN amma ko Akanta Janar bai da labarin an yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wani darekta a Ma’aikatar tattalin arziki ya bada shaida a kotu a shari’ar da ake yi da Godwin Emefiele da EFCC.

Babban jami’in ya yi wa kotun tarayya mai zama a Abuja bayanin yadda aka cire N124.86bn daga babban bankin kasa.

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele da Muhammadu Buhari lokacin da bankin CBN ya canza kudi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

EFCC ta kira shaidu 10 a shari'ar Emefiele

The Cable ta ce Ali Mohammed ya bayyana a kotu a matsayin shaida na 10 da hukumar EFCC ta kawo domin ta kafa hujja.

Kara karanta wannan

Iyaye sun shiga ha’ula’i, ‘yan bindiga sun bukaci N950m kafin sakin masu NYSC

Ali Mohammed ya ce Ma’aikatar kudi da Ofishin Akanta Janar na kasa ba su da masaniya game da kudin da aka cire.

Babban lauyan da ya tsaya wa EFCC a kotun tarayyan, Abbas Mohammed ne ya jagoranci Ali domin ya bada shaida.

Yadda aka fara jin labarin an cire kudi a CBN

Jami’in yake cewa sun fahimci an cire kudin ne bayan samun wata wasikar bincike da ta sanar da su cewa an cire wasu kudi.

Darektan ya ce sai ya tuntubi sauran ma’aikata domin jin ko suna da labarin an dauki wadannan biliyoyi daga asusun CBN.

A cewarsa, duk ma'aikatan sun sanar da shi cewa ba su da labarin an cire makudan kudin.

Daga nan sai ya rubuta wa babban sakataren ma’akatarsa ta ofishin Akanta Janar domin ya ji ko sun san da labarin tafiyar kudin.

The Guardian ta rahoto shaidan yana cewa Akanta Janar ma ya ce bai san an yi ba, suka ce kai tsaye bankin ya dauki kudin.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

EFCC ta samu bayanin da ta nema

Da ya samu wannan bayani sai darektan ya iya amsa wasikar da EFCC ta rubuto masu.

An kuma yi amfani da wasikun da aka rika aika wa da su tsakanin hukumar EFCC zuwa ofishin darektan a matsayin hujjoji.

An yi wa alkali bayani game da irin wannan cire kudi da ake yi wanda bai da alaka da aikin wani ofishi a gwamnatin Najeriya.

Rahoton ya ce a ka’idar aiki, ya kamata OAGF ya samu labari idan an cire kudi irin haka.

Lauyan da yake kare wadanda ake kara, Olalekan Ojo, ya nuna bai da adawa da wannan karin hujja da aka gabatar a kan su.

Godwin Emefiele
Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a cikin kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An zargi Emefiele da tura wa matarsa kudi

An ji yadda aka zargi Godwin Emefiele da tura kudin bankin CBN zuwa asusun matarsa, Margaret Emefiele da wasu kamfanoni.

Shaidar EFCC, Ifeoma Ogbonnaya wacce ma'aikaciyar banki ce, ta bayyana cewa ta samu umarni daga matar a tura wasu kudi.

Kara karanta wannan

An kama shugaban ƙungiyar magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso

EFCC tana zargin Emefiele da laifin almundahana da kuma ba da kwangiloli ga kamfanonin matarsa da 'yan uwanta da yake ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng