ADC Za Ta Yi wa INEC Kishiya wajen Tattara Kuri’u da Sakin Sakamakon Zabe a 2027

ADC Za Ta Yi wa INEC Kishiya wajen Tattara Kuri’u da Sakin Sakamakon Zabe a 2027

  • ADC ta ce za ta tattara tare da wallafa sakamakon zabe daga rumfunan zabe da kanta a babban zaben 2027
  • Kakakin jam’iyyar hamayyar, Blolaji Abdullahi ya yi bayanin yadda za su samu sakamakon zabe a fadin kasar
  • Ya fitar da sanarwa yana mai cewa yin hakan yana cikin hakkokin da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jam’iyyar ADC ta ce ita da kan ta za ta tattara kuri’un da aka kada mata a lokacin zaben shekarar 2027.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta ce tattarawa da wallafa sakamakon zaben da za ta yi yana cikin damar da ta ke da ita.

INEC.
Ma'aikatan INEC lokacin zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jam'iyyar ADC ta ba hukumar INEC amsa

ADC ta bayyana hakan ne a martaninta ga jan kunnen da aka ce ya fito daga Shugaban Hukumar INEC in ji The Sun.

Kara karanta wannan

Labaran bogi da suka rika yawo a kafafen sada zumunta a makonnin nan

Farfesa Jaosh Amupitan ya yi gargadi game da yada sakamakon zaben da aka tattara ba tare da izinin hukumar ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ADC ya nuna za su kishiyanci INEC.

Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar za ta rubuta sakamakon zaɓe ta hannun wakilanta da ke rumfunan zabe a kasar.

Sanarwar ta ce:

“ADC za ta yada sakamakon zaben da ta tattara ga jama’a. Wakilanmu za su rubuta sakamakon, rassan jam’iyyar za su tattara su, sannan mu sanar da jama’a sahihan alkaluma, tare da bayyana inda suka fito da matsayin ingancinsu.”

ADC tana da ikon wallafa sakamakon zabe?

Jam’iyyar ta dogara ne da damar fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada wajen yin wannan karfin hali.

Kakakin jam’iyyar adawar ya yarda babu wanda doka ta ba ikon sanar da sakamakon zabe illa hukumar INEC ta kasa.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi wa APC tonon asiri, ya ce ta kawo sabuwar dabara a 2027

Premium Times ta rahoto shi ya ce hakan ba ya hana jam’iyyun siyasa da ’yan kasa tattara bayanan zabe da yada wa mutane.

“Muna sane da hakkinmu na faɗin albarkacin baki a karkashin kundin tsarin mulki. Haka kuma, muna sane da iyakokin da ke tattare da waɗannan hakkoki.
Muna kuma da yakinin cewa wadannan iyakoki ba su soke hakkinmu na tattarawa da yada sakamakon zabe ba.”

Me doka ta ce game da yunkurin ADC?

Jaridar ta ce yancin fadin albarkacin baki yana cikin Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Haka kuma, Dokar zabe ta tanadi matakan da za a bi wajen kirga kuri’u, rubuta sakamako, tattara shi da yada wa jama'a.

Wakilan ’yan takara da jam’iyyun siyasa da ke rumfunan zaɓe suna da haƙƙin karɓar sakamako bisa tanadin dokar kasa.

Amma a dokar zabe, sakamakon da jam’iyyu suka tattara da kansu ba ya maye gurbin aikin INEC.

Atiku
'Dan takaran ADC a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar da wasu 'yan adawa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Dan takaran ADC ya hada APC da mahaukata

Mahaukata da barayi ne kawai za su sake zabar Shugaba Bola Tinubu kamar yadda aka rahoto Rotimi Amaechi yana fada a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC

A zaben shekara ta 2027, Amaechi yana so jama’a su dangwala kuri’arsu ga jam’iyyar ADC da 'dan takaranta, Alhaji Atiku Abubakar.

Bayan sukar mulkin APC, tsohon Ministan Sufurin ya ce gwamnatin Tinubu ba ta yin aiki sai idan ta ga kudi za su shigo aljihunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng