Ba Boye Boye: Tinubu Ya Fadi Kalibar da Ya Ji Haushi Ta Ki Zaben Shi a 2023

Ba Boye Boye: Tinubu Ya Fadi Kalibar da Ya Ji Haushi Ta Ki Zaben Shi a 2023

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya ji haushi lokacin da wasu ’yan ƙabilar Igbo suka ƙi zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Ya buƙaci ’yan ƙabilar da ke zaune a Legas da su mara masa baya a zaɓen 2027, yana mai cewa ya kamata su rama ƙoƙarin gwamnatinsa
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin Igbo, ’yan kasuwa, matasa da sauran masu ruwa da tsaki a cibiyar Wole Soyinka a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya ji haushi da wasu ’yan ƙabilar Igbo da ke zaune a Legas saboda yadda suka ƙi zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa da shugabannin Igbo, ’yan kasuwa, matasa da sauran masu ruwa da tsaki a cibiyar Wole Soyinka da ke Iganmu, Legas.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya a wajen kamfen a Jigawa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

TheCable ta ruwaito cewa Tinubu ya yi amfani da taron wajen neman goyon bayan al’ummar Igbo domin sake zaɓensa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Tinubu na son goyon bayan Igbo

Da yake magana da mahalarta taron, shugaban ya ce duk da cewa ya ji haushi kan yadda wasu daga cikinsu suka ƙi zaɓensa a 2023, yanzu an sasanta, don haka ya kamata su fito su kaɗa ƙuri’unsu a zaɓe mai zuwa.

Ya ce:

“Wasunku ba su zaɓe ni ba a 2023, na ji haushi fa, amma yanzu mun sasanta. Ku samo katin zaɓenku, za ku zaɓe ni a wannan karon. Idan ranar zabe ta zo, ku fito ku kaɗa ƙuri’a. Alkawari alkawari ne, Bola Tinubu yana APC.”

Tinubu ya kuma buƙaci ’yan Igbo da ke Legas su zaɓe shi, ɗan takarar gwamnan APC, Obafemi Hamzat, da sauran ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Me ya faru a zaɓen 2023 a Legas?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu matsala yana aske gemu a fadar shugaban kasa

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ɗan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi, ya doke Tinubu a jihar Legas, duk da cewa jihar ta kasance cibiyar siyasarsa tsawon shekaru.

Obi ya samu ƙuri’u 582,454, yayin da Tinubu ya samu 572,606, wanda ya ba ɗan takarar LP nasara da tazarar ƙuri’u 9,848.

A lokacin zaɓen, ƙungiyar Obidient Movement ta samu goyon bayan matasa da mazauna birane, ciki har da wasu daga cikin al’ummar Igbo da ke Legas.

Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso
Dan takarar NDC a 2027 Peter Obi NDC da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

Sai dai goyon bayan Obi bai tsaya ga ’yan Igbo kaɗai ba, domin ya samu ƙuri’u daga mutane masu bambancin ƙabila da addini.

Za a yi zaben gwaji

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,676 domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da loda sakamakon zaɓe ta intanet.

Hukumar ta ce za a gudanar da gwajin ne a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba guda 8,838 da ke faɗin Najeriya.

INEC ta bayyana cewa manufar gwajin ita ce tantance ingancin na’urar BVAS, duba hanyoyin tantance masu zaɓe da gano matsalolin fasaha da ka iya tasowa kafin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng