Kamfanin Maggi Ya Kaddamar da Sababbin Jakadu a Najeriya

Kamfanin Maggi Ya Kaddamar da Sababbin Jakadu a Najeriya

MAGGI ya kaddamar sababbin jakadu biyar da suka hada da Bimbo Ademoye, ya yi bikin haɗin gwiwa da masu ƙirƙira a taron creators’ conference na 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Taron na kwanaki biyu mai taken “Stars Are Forever” ya kasance wani ɓangare na bikin cika shekaru 60 da MAGGI ya yi a Najeriya.

Maggi ya kaddamar da jakadu
Jakadun da kamfanin Maggi ya kaddamar Hoto: Maggi
Source: Facebook

Kamfanin na MAGGI ya tarbi jarumar fina-finai Bimbo Ademoye, tauraron shirin talabijin kuma ɗan wasa Neo Akpofure, Chef Alams da Nahna Amy, da Kilani Latifat Omowunmi (Pot of Flavors) a matsayin sababbin jakadun da za su zama alamar kasuwancinta.

Wannan dai na cikin ayyukan da aka gudanar a taron masu kirkira na MAGGI Creators’ Conference da aka yi a ranar 13 da 14 ga watan Nuwamban 2026.

Ƙarin waɗannan muhimman mutanen biyar dai na da nufin faɗaɗa yawan ƙirƙirar da MAGGI ke da su, waɗanda suka haɗa da ƙwararrun masu ƙirƙirar da fitattun mutane a kafafen sadarwa na zamani.

Haka kuma, kamfanin ya sabunta haɗin gwiwarsa da kusan jakadu 12 da yake aiki da su a baya, domin ƙarfafa dangantakar da yake da ita da masu ƙirƙira da yake mu’amala da su.

Kara karanta wannan

Mutane suna shan wahala a kasa, Tinubu ya shirya kawo sauki ta hanyar sufuri

An bayyana sababbin jakadun ne a yayin taron na kwanaki biyu mai taken “Stars Are Forever”, wanda ya kasance wani ɓangare na bikin cika shekaru 60 da MAGGI ya yi a Najeriya.

Taron ya haɗa mutanen ne domin tattauna damar da ake da ita a fannin ƙirƙira, haɗin gwiwar kasuwanci da gina kasuwanci mai ɗorewa a cikin tattalin arzikin masu ƙirƙira da ke bunƙasa a Najeriya.

Sababbin jakadun dai sun fito ne daga fannoni daban-daban na nishaɗi, salon rayuwa da ƙirƙira, abin da ke nuna ƙoƙarin MAGGI na isa ga jama’a masu yawa ta hanyar jakadun, wadanda suka fito daga fannoni daban-daban da masu amfani da kayayyakin kamfanin.

Baya ga ƙaddamar da sabbin jakadu da kuma murnar haɗin gwiwar, taron ya samar da dandalin tattaunawa kan yadda masu ƙirƙira za su iya mayar da ƙwarewarsu da tasirinsu a intanet zuwa kasuwanci mai amfani, musamman a lokacin da ƙarin ’yan Najeriya ke binciken hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta hanyar kirkira a kafafen sadarwa na zamani.

Da take jawabi a wurin taron, Manajar Bangaren Sinadin Girki na MAGGI a kamfanin Nestlé Nigeria, Funmi Osineye, ta bukaci masu ƙirƙira su duba aikinsu da cikakkiyar fahimtar damarrmakin kasuwanci da ke gabansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Legit.ng Branded Content avatar

Legit.ng Branded Content (marketing page) This account is used for publishing branded/sponsored content. For any enquiries please email: ads@corp.legit.ng or call: +234 810 304 48 99