'Yan APC Sun Yi Hadari a Hanyar Kamfen, kusan Mutum 20 Sun Mutu

'Yan APC Sun Yi Hadari a Hanyar Kamfen, kusan Mutum 20 Sun Mutu

  • Mutum 15 da ke goyon bayan jam’iyyar APC a jihar Zamfara sun mutu a wani mummunan hatsarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron yaƙin neman zaɓe
  • Masu goyon bayan jam’iyyar na tafiya ne daga Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar ƙaddamar da gangamin zaɓe lokacin da hatsarin ya rutsa da su
  • Saboda rasuwarsu, kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamnan APC a Zamfara ya ɗage gangamin da aka shirya gudanarwa a Maru ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta ɗage gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna da aka shirya gudanarwa a ƙaramar hukumar Maru, bayan mutuwar magoya bayanta 15 a hatsarin mota.

Hatsarin ya rutsa da magoya bayan ne yayin da suke tafiya daga Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar taron ƙaddamar da gangamin zaɓe.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake dawo da alkawarin da ya dauka a baya, ya roki yan Najeriya

Gwamna Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen ne ya sanar da ɗage taron a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan Litinin, wadda babban sakatarensa, Abubakar Nakwada, ya sanya wa hannu.

'Yan APC 15 sun mutu

Sanarwar ta ce mutane 15 sun rasa rayukansu a hatsarin, yayin da wasu da dama suka samu raunuka kuma suke karɓar kulawar likitoci.

Kwamitin ya bayyana alhini kan rasuwarsu, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansu, al’ummar Gummi da sauran mazauna jihar Zamfara.

Ya kuma ce yana bibiyar halin da waɗanda suka jikkata suke ciki, kuma zai samar da tallafin da ya dace ga waɗanda suka tsira da kuma iyalan mamatan.

An ɗage gangamin Maru

Kwamitin ya ce an ɗage gangamin da aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026, domin nuna girmamawa ga waɗanda suka rasu da kuma tausaya wa iyalansu.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da sabon jadawalin gangamin yaƙin neman zaɓen nan gaba.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da cikas, kotu ta kori mutumin Atiku da ke takarar gwamna

Taswirar jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Najeriya.
Source: Original

Haka kuma, kwamitin ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan, ya shigar da su Aljannatul Firdaus, sannan ya ba waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa da iyalansu haƙurin wannan rashi.

Baya ga mutuwar magoya bayan APC a hatsarin, kwamitin ya kuma yi alhinin rasuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe, wanda ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

An raba motocin tallata Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar Tinubu Again Movement, mai samun goyon bayan ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ta bayyana shirinta na tara ƙuri’u miliyan 20 a 2027.

Ƙungiyar ta kuma sanar da shirin bayar da tallafin fara sana’a ga mutane 20,000 da kuma rabon motoci da babura 1,000 ga ’yan Najeriya.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da ƙungiyar a Abuja, inda ya ce an tsara dabarun tattara magoya baya a faɗin ƙasar domin cimma burin da suka sanya a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng