"Alamu da Lissafin Siyasa Sun Nuna Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027"
- Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC za su yi nasara a babban zaben 2027
- Dan majalisar ya yi watsi da ikirarin cewa Tinubu na rasa farin jini a Arewacin Najeriya, yana mai cewa har yanzu yana da magoya baya da yawa a yankin
- Jibrin ya kara da cewa Arewacin Najeriya na da dalilai da dama na goyon bayan Tinubu ya zarce wa'adi na biyu a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jigo a APC daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar za su lashe zaben 2027, yana mai cewa babu fargaba a tsakaninsu.
Ya ce dukkan alamu da lissafe-lissafen siyasa na nuna cewa APC da Tinubu za su samu nasara a zaben mai zuwa, inda shugaban kasar ke neman zarcewa karo na biyu.

Source: Facebook
Jibrin, wanda yake wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a Majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television.
“APC ba ta cikin fargaba, ko kadan ba mu cikin fargaba. Muna da kwarin gwiwar cewa za mu lashe zaben.
"A matsayinka na Musulmi, kana son sanya Allah cikin lamarin, amma ina gaya maka cewa ko da ta fuskar lissafin dan Adam, dukkan alkaluma da lissafe-lissafe suna nuna APC da Shugaba Bola Tinubu ne za su yi nasara,” in ji Jibrin.
Jibrin ya tabo batun farin jinin Tinubu
Dan majalisar ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Tinubu na rasa farin jini a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana cewa faifan bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka nuna wasu mutane suna ihun “ba ma yi” yayin da ayarin motocin shugaban kasa ya wuce, mai yiwuwa an kirkire shi ne ta amfani da fasahar zamani ta AI.
Ya ce bai kamata a yi amfani da abin da ya faru a wuri guda wajen tantance yadda shugaban kasa ya ke da farin jini a daukacin Arewacin Najeriya ba.
A cewarsa, Tinubu na da magoya baya da yawa a yankin fiye da masu adawa da shi.

Source: Twitter
Dalilan Arewa na sake goyon bayan Tinubu
Jibrin ya kara da cewa Arewacin Najeriya na da dalilai da dama na goyon bayan Tinubu a zaben 2027, bisa la’akari da irin gudunmawar da ya ce shugaban kasar ya bayar wajen ci gaban yankin a tsawon shekaru.
“Idan aka yi la’akari da dukkan abubuwan da ya yi wa Arewa a shekarun da suka gabata da kuma abin da yake yi wa yankin a yanzu, Arewa na da dukkan dalilan da za ta goyi bayan Shugaba Bola Tinubu,” in ji shi.
An bukaci Arewa ta goyi bayan Tinubu
Kun ji cewa shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, ya yi kira ga al'ummar Arewa da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a 2027.
Dan majalisar ya bayyana cewa damar shugabancin Najeriya za ta koma hannun Arewa ne bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Asali: Legit.ng

