Pantami Ya Rikita Lissafin APC, 'Yan Acaba Sun Ce Gombe sai Malam
- Kungiyar ’yan achaba a Jihar Gombe ta gudanar da wani taron nuna goyon baya ga Farfesa Isa Ali Pantami a birnin Gombe
- Mambobin kungiyar daga sassa daban-daban na jihar sun hallara a Pantamiyya Square domin bayyana matsayinsu kan tafiyar Pantami
- Shugabannin kungiyar sun ce za su ci gaba da wayar da kan sauran ’yan achaba da jama’a tare da gudanar da ayyukansu cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Kungiyar ’yan achaba a Jihar Gombe ta jaddada goyon bayanta ga Sheikh Isa Ali Pantami, yayin da mambobinta suka gudanar da wani taro a birnin Gombe.
An gudanar da taron ne a yammacin Talata, 22 ga Satumba, 2026, a Pantamiyya Square, inda ’yan achaba daga sassa daban-daban na jihar suka hallara.

Source: Facebook
’Yan achaba suna tare da Pantami
A bidiyon da dan takarar ya wallafa a Facebook, shugabanni da wakilan kungiyar sun ce sun shirya taron ne domin sake bayyana goyon bayansu ga Farfesa Pantami.
Sun kuma bayyana aniyarsu ta ci gaba da kasancewa tare da tafiyar Pantami tare da karfafa alaka tsakanin mambobin kungiyar da sauran magoya baya.
Masu jawabi a wajen taron sun bayyana dalilan da suka sa suke goyon bayan Farfesa Pantami, tare da bayyana irin shugabancin da suke fatan gani a Jihar Gombe.
Kungiyar ta yi kira ga mambobinta
A yayin taron, mambobin kungiyar sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da wayar da kan sauran ’yan uwansu da jama’a kan matsayinsu.
A bayanan da suka yi, sun kuma jaddada cewa za su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da bin doka da oda.
'Yan APC sun koma PDP
A wani labarin, kun ji cewa Hon. Ibrahim Adamu Muhammad, wanda aka fi sani da Uban Dawakin Gombe, da Alhaji Auwalu Alhassan, wanda aka fi sani da Chiburosi, sun fice daga APC zuwa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya.
Ibrahim Adamu Muhammad ya taba zama mataimakin shugaban Karamar Hukumar Gombe, yayin da Auwalu Alhassan ya taba zama shugaban kungiyar masu nika man gyada ta Jihar Gombe.
Sanarwar da Pantamiyya Movement ta fitar ta ce mutanen biyu sun bayyana amincewarsu da kwarewar Pantami, gaskiyarsa, iya shugabanci da kuma iliminsa kan harkokin gwamnati da ci gaban al’umma.

Source: Facebook
Pantami ya kara samun karfi
A cewar sanarwar, sauyin jam’iyyar na Ibrahim Adamu Muhammad da Auwalu Alhassan ya kara wa PDP da tafiyar Pantami karfi a fadin Jihar Gombe.
Sanarwar ta kuma ce sun shiga PDP ne tare da mara wa Pantami baya, da kuma jagoran jam’iyyar a jihar, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar.
An nada jami’an gwamnati a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya amince da nadin kwamishinoni uku, masu ba shi shawara na musamman biyu da manyan mataimaka na musamman hudu.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce gwamnan ya aika sunayen wadanda aka zaba a matsayin kwamishinoni zuwa Majalisar Dokokin Jihar.
Kwamishinonin da aka zaba su ne Dr Ahmed Wali Doho, Nasiru Adamu Degri da Dr Muhammad A. Bello, yayin da Abdulmalik Jibrin da Mohammed Nuhu aka nada masu ba gwamnan shawara na musamman.
Asali: Legit.ng

