Kwana Ya Kare: Tinubu Ya Aika Sako da Aka Sanar da Rasuwar Tsohon Gwamna a Najeriya
- Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris
- Tinubu ya yaba da gudunmawar tsohon gwamnan wajen ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya da kuma shekarun da ya shafe yana yana hidima
- Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya bai wa iyalan marigayin ƙarfi da juriyar jure wannan babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matuƙar alhini bisa rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, wanda ya rasu a kasar Birtaniya.
An tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, 2026, yana da shekaru 77 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi rashi," Ododo ya yi alhini da aka tabbatar da rasuwar tsohon gwamna a Najeriya

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya nuna alhini bisa wannan rashi a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin, 21 ga Satumba, 2026.
Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya
A cikin sanarwan, Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Ibrahim Idris, gwamnatin da al’ummar Jihar Kogi, da abokai, makusanta da abokan siyasar marigayin.
Shugaban ya bayyana rasuwar Alhaji Idris a matsayin babban rashi ga Jihar Kogi da Najeriya baki daya.
Ya kuma bayyana cewa tsohon gwamnan ya sadaukar da wani babban bangare na rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima da kuma ci gaban jiharsa.
Alhaji Ibrahim Idris ya kasance Gwamnan Jihar Kogi daga shekarar 2003 zuwa 2011. Gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman sassa.

Kara karanta wannan
Mai alfarma Sarkin musulmi ya yi babban rashi, Hajiya Nana Asma'u ta riga mu gidan gaskiya
Tinubu ta tuna gudummuwar marigayin
Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar tsohon gwamnan wajen ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya da kuma shekarun da ya shafe yana taka rawa a harkokin gwamnati.
Tinubu ya ce:
“Alhaji Ibrahim Idris ma’aikacin gwamnati ne mai kishin yi wa jama’a hidima, kuma shekarun da ya yi yana kan mulki sun kasance wani muhimmin babi a tarihin siyasa da ci gaban Jihar Kogi.
“Rasuwarsa babban rashi ne mai raɗaɗi ga iyalansa, Jihar Kogi da Najeriya baki daya. A wannan lokaci mai wahala, dole ne mu tuna tare da girmama gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jiharsa da ƙasarmu."
“Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa da al’ummar Jihar Kogi. Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.”
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya bai wa iyalan marigayin ƙarfi da juriyar jure wannan babban rashi da suka yi.

Source: Facebook
Gwamna Ododo ya ayyana zaman makoki
Kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamna, Alhaji Ibrahim Idris, yana da shekaru 77 a wani asibiti da ke Birtaniya
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin girmama marigayin, sannan ya bayar da umarnin sauke tutar Najeriya da ta jihar Kogi zuwa rabi a dukkan ofisoshin gwamnati da cibiyoyi a tsawon lokacin.
A cikin sanarwar, Gwamna Ododo ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar tsohon gwamnan, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga jihar Kogi da Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng
