‘Arewa Ta Tinubu Ce’: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Bangaren da Rarara Ya Yi Fice

‘Arewa Ta Tinubu Ce’: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Bangaren da Rarara Ya Yi Fice

  • Fadar shugaban kasa ta yabawa sabon wakar yakin neman zaben Tinubu da mawakin siyasa Rarara ya fitar
  • Bayo Onanuga ya ce APC na kara samun karbuwa da gudanar da yakin neman zabe a Arewa da sauran sassan Najeriya
  • Sabuwar wakar ta jawo ra'ayoyi mabambanta a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yabawa, wasu ko ke ganin tasirinsa ya Rarara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yaba da sabuwar wakar yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka Dauda Kahutu Rarara ya fitar.

Fadar ta bayyana haka ne tare da yabawa tasirin wakokin da fitaccen mawakin siyasar Hausa domin nuna goyon baya ga shugaban kasar gabanin zaben 2027.

An yabawa Rarara kan tallata Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara. Hoto: @omonlakiki.
Source: Twitter

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a,

Kara karanta wannan

Bayan tara malamai 2000, Barau Jibrin ya haɗa kan sarakuna 3000 saboda Tinubu da Abba

Yadda gwamnatin Tinubu ya yabawa Rarara

Onanuga ya bayyana wakar a matsayin wata sabuwar wakar goyon bayan Tinubu daga Arewacin Najeriya.

Onanuga ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda jam'iyyar APC ke kara fadada yakin neman zabenta, yana mai cewa jam'iyyar ta karya hasashen masu cewa ba za ta iya gudanar da yakin neman zabe a Arewa ba.

Ya ce tun da farko wasu na yada cewa APC ba za ta iya gudanar da gangamin siyasa, kafa allunan tallace-tallacen yakin neman zabe ko sanya alamomin jam'iyyar da na Asiwaju a yankin Arewa ba.

Sai dai Onanuga ya ce yadda jam'iyyar ke gudanar da yakin neman zabenta a yanzu ya nuna akasin wannan batu, ba a Arewa kadai ba, har ma a sauran sassan Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya kuma yi hasashen cewa Tinubu zai samu nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairun 2027.

Kara karanta wannan

Bangare 1 da Bola Tinubu ya yi wa Atiku da Peter Obi fintinkau a siyasa

Bidiyon ya nuna yadda wakokin yakin neman zabe ke yaduwa a kafafen sada zumunta, tare da yadda magoya bayan 'yan siyasa ke karbarsu yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi gabanin zaben 2027.

An yabawa tasirin Rarara a Arewa
Mawakin siyasa na jam'iyyar APC a Arewacin Najeriya.. Dauda Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Tasirin Rarara a siyasar Arewa

Rarara ya kasance daya daga cikin fitattun mawakan siyasar Hausa a Arewacin Najeriya, musamman saboda wakokin da ya rika yi wa APC da manyan 'yan siyasar jam'iyyar.

Mawakin ya samu karbuwa a fadin Najeriya sakamakon wakokin siyasa da ya rika yi domin tallata tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabukan 2015 da 2019.

Tasirin wakokinsa ya ci gaba a gwamnatin Tinubu, inda ya fitar da wakoki da dama domin nuna goyon baya ga Tinubu, ciki har da shahararriyar wakarsa mai suna Omo Ologo, kalma ce ta Yarbanci da ke nufin mutum mai daukaka ko sa'a.

Sai dai wakokin siyasar Rarara sun sha fuskantar suka, musamman idan ya yi amfani da kalamansa wajen sukar 'yan adawa da wasu fitattun mutane.

Hadimin Atiku ya magantu kan farmakin Rarara

A baya, mun ba ku rahoton cewa tawagar Atiku Abubakar ta yi martani bayan wasu fusatattun mutane sun far wa mawakin yabon Tinubu, Dauda Kahutu Rarara, a Abuja.

Kara karanta wannan

Makinde ya shirya marawa Atiku baya a zaɓen 2027? An samu bayanai

Mai magana da yawun Atiku ya ce goyon bayan da Rarara ke bai wa shugaban ƙasa haƙƙinsa ne na dimokuraɗiyya.

Paul Ibe ya bayyana cewa siyasa ta fara nuna Tinubu na zama nauyi ga Rarara, duk da cewa ya yi Allah-wadai da harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.