Gwamna Ya Dauki Zafi da Yan Bindiga Suka Shiga Gari, Suka Kashe Basarake a Najeriya
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Lafagu, inda suka kashe basaraken ƙauyen tare da tilasta wa mazauna gudun hijira zuwa wuraren da suka fi aminci
- Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya yi Allah-wadai da kisan basaraken, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci
- Gwamnatin jihar Kebbin ta tabbatar da cewa tana aiki da jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun tayar da hankula tare da tarwatsa mazauna ƙauyen Lafagu da ke ƙaramar hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi a yammacin Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe dagacin ƙauyen, Alhaji Saidu Mujeli, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa wuraren da suka fi aminci.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Facebook
Gwamna Nasir ya yi Allah-wadai
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kebbi, Comrade Dr Nasir Idris, ya yi Allah-wadai da kisan basaraken da yan ta'addan suka yi, yana mai bayyana lamarin a matsayin dabbanci.
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Ahmed Idris, ya sanya wa hannu tare da rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya bayyana alhininsa kan lamarin da ya faru a ƙauyen Lafagu, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da kuma raba mazauna yankin da muhallansu.
Matakin da gwamnatin Kebbi ta dauka
Gwamna Idris ya tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa cewa gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin gano tare da kama waɗanda ke da hannu a hare-haren, sannan a gurfanar da su a gaban doka.
Ya bayyana cewa ana ƙara ƙaimi tare da hukumomin tsaro da abin ya shafa domin ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan da abin ya shafa da kuma kare rayuka da dukiyoyin mazauna.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun mamaye gidan kwamishina, sun bude wuta ba tare da nuna tausayi ba
Gwamnan Kebbi ya yiwa basaraken addu'a
Gwamna Nasir Idris ya ce bai ji dadin kisan basaraken ba, amma gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai ta farauto tare da tabbatar da an hukunta duk masu hannu a wannan ta'addanci ba.
Gwamnan ya ce:
“Na karɓi labarin abubuwan da suka faru a kusa da Kaoje cikin matuƙar baƙin ciki da damuwa, musamman a al’ummomin Lafagu da Buya.
"Lamarin ya yi sanadin asarar rayuka, ciki har da rasuwar dagacin kauyen Lafagu, Alhaji Saidu Mujeli. Allah SWT Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.”

Source: Original
Yan sanda da sojoji sun samu galaba
Kun ji cewa rundunar ’yan sandan Kebbi ta ce an kashe ’yan bindiga da dama a dajin Gumki da ke yankin Kangiwa a jihar ta Arewa maso Yamma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda reshen jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.
Ya ce rundunar haɗin gwiwar sojoji da yan sanda ta yi nasarar fafatawa da ’yan bindigan tare da kashe da dama daga cikinsu yayin gudanar da samamen.
Asali: Legit.ng