Kaico: An Kashe Budurwa a Gidan Saurayinta kan Rikicin Daukar Cutar Kanjamau, HIV
- An kama wani matashi, Emmanuel Okpara, dan shekara 30 bisa zargin kashe budurwarsa kan sabanin daukar cutar kanjamau a jihar Enugu
- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Enugu
- Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar, Mamman Giwa, ya umarci Sashen Binciken Laifuffuka na Jiha (SCID) da ya gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Nigeria - Rundunar 'Yan Sandan Jihar Enugu ta tsare wani mutum mai shekaru 30, Emmanuel Okpara, wanda ke zaune a Unguwar Olympic Layout a Enugu, bisa zargin kashe budurwarsa mai suna Chinyere.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Enugu kuma ya rarraba wa manema labarai a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Source: Twitter
Ndukwe ya bayyana cewa har yanzu ba a tantance sunan mahaifin Chinyere, shekarunta, da adireshinta ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda saurayi ya kashe budurwa a Enugu
Ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda dake karkashin ofishinnAwkunanaw ne suka ceto wanda ake zargin daga hannun fusatattun jama’a tare da tsare shi da misalin karfe 6:30 na yamma a ranar 21 ga Satumba, 2026.
“Binciken farko ya nuna cewa ana zargin saurayin ya kashe budurwarsa a ranar 19 ga Satumba, inda ya nannaɗe gawarta a cikin leda sannan ya kulle ta a cikin banɗakin gidansa.
“Daga bisani, karni da warin da gawar ke yi saboda fara rubewa ya jawo hankalin makwabta, wadanda suka fasa kofa sannan suka kama shi kafin isowar jami'an 'yan sanda.
“An kwashe gawar zuwa dakin adana gawa domin gudanar da gwajin tabbatar da dalilin mutuwa, yayin da ake ci gaba da kokarin zakulo tare da sanar da 'yan uwanta,” in ji sanarwar.
Abin da ya hada masoyan rigima
Sanarwar ta kara da cewa yayin tambayoyin farko da aka yi masa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Ndukwe ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa cewa lamarin ya faru ne sakamakon wani sabani da aka samu tsakaninsa da marigayiyar game da zargi kan wane ne ya sanya wa dan uwansa da cutar kanjamau (HIV).
Ya kara da cewa a yayin musayar kalaman, Okpara ya doki marigayiyar a kai da tabarya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Matakin da yan sanda suka dauka
A cewar Premium Times, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Enugu, Mamman Giwa, ya umarci Sashen Binciken Laifuffuka na Jiha (SCID) da ya gudanar da binciken kwakwaf domin gano cikakkun bayanai game da lamarin.

Source: Original
Kwamishinan ya umarci sashen na SCID da ya tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Sannan ya gargadi jama'a, musamman matasan yan mata, da su rika sanar da 'yan uwansu ko abokan da suka yarda da su game da wuraren da za su je.

Kara karanta wannan
Zargin cin kudi ya kai ‘dan takaran APC a zaben majalisa cikin ragar hukumar ICPC
Matashi ya kashe budurwa a Kaduna
Kun ji cewa Rundunar ’Yan sanda a Kaduna ta kama wani mutum kan zargin kashe budurwarsa a karamar hukumar Chikun.
Rundunar ta ce wanda ake zargin shi ne mutum na ƙarshe da ya yi hulɗa da marigayiyar kafin a gano gawarta a yankin Romi, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.
Asali: Legit.ng
