Gombe 2027: Sakon Jamilu Gwamna ga Pantami, ADC Ana daf da Fara Kamfen

Gombe 2027: Sakon Jamilu Gwamna ga Pantami, ADC Ana daf da Fara Kamfen

  • Dan takarar gwamnan Gombe na APC, Jamil Gwamna, ya shawarci sauran yan takarar da ke sauran jam'iyyu a jihar
  • Gwamna ya ce yakin neman zabensa zai mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki, noma, lafiya, ilimi da karfafa matasa
  • Ya bukaci al’ummar Gombe su zauna lafiya, tare da fifita muradun jihar kan bambance-bambancen siyasa, yayin da yake shirin bayyana cikakken tsarinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Dan takarar jam’iyyar APC na kujerar gwamnan Gombe, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, ya yi magana ana daf da fara kamfe.

Jamilu Gwamna ya bukaci ‘yan siyasa da mazauna jihar su rungumi yakin neman zabe mai tsafta, mutunci da magana kan muhimman batutuwa.

Jamilu Gwamna ya shawarci yan takara
Jamilu Gwamna, wanda ya zama dan takarar gwamnan APC a jihar Gombe ta tsarin sulhu Hoto: Dr. Jamilu Isyaku Gwamna.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Sani Shawai, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

'Abin da ƴan Gombe suka cancanta a siyasa'

Gwamna ya ce al’ummar Gombe sun cancanci yakin neman zabe da zai mayar da hankali kan damuwarsu, bukatunsu da burinsu, maimakon cin mutunci, kai hare-haren kashin kai da abubuwan da za su dauke hankali.

Dan takarar APC ya ce yakin neman zabensa zai kasance na jama’a, mai samar da mafita kuma mai mayar da hankali kan gabatar da dabarun ci gaban jihar.

Ya ce:

“Tun daga farko, na bayyana cewa zan gudanar da yakin neman zabe bisa tsari da manufofi, ba ni da sha’awar siyasar cin mutunci, suka na kashin kai da abubuwan da ba su da muhimmanci."

Gwamna ya ce akidar “Gombe Sama da Komai” za ta kasance ginshikin da zai jagoranci yakin neman zabensa a zaben gwamnan jihar na 2027.

Ya bayyana samar da ayyukan yi, bunkasar tattalin arziki, karfafa matasa da mata, bunkasa noma da kiwo, ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa a matsayin muhimman batutuwan yakin neman zabensa.

Kara karanta wannan

Ainihin dalilin gwamna Nasir Idris na sauya mataimakinsa a 2027

Jamilu Gwamna ya barranta kansa da siyasar cin mutunci
Gwamna Inuwa Yahaya lokacin da ya daga hannun Jamilu Gwamna, da tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami Hoto: Dr. Jamilu Isyaku Gwamna, Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Jamilu ya bukaci mata wa Tinubu baya

Dan takarar APC ya kuma bukaci mazauna jihar su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a yunkurinsa na neman kujerar Sanata, da sauran ‘yan takarar APC.

A cewarsa, ayyuka, shirye-shirye da tsare-tsaren gwamnatin Inuwa Yahaya sun nuna jajircewar APC wajen kawo ci gaba da ingantaccen shugabanci a Gombe.

Gwamna ya ce zai bayyana cikakken tsarin tafiyar da jiharsa ga jama’a ne bayan fara yakin neman zaben kujerar gwamna da na Majalisar Dokokin jihar a hukumance.

Ya ce hakan zai yiwu ne idan jihar ta samu shugabanci mai hangen nesa, ingantaccen tsarin tafiyar da gwamnati da kuma hadin kan jama’a.

Saboda haka, Gwamna ya bukaci ‘yan siyasa, magoya baya da sauran ‘yan kasa su kiyaye zaman lafiya, tare da gudanar da yakin neman zabe cikin mutunci da ladabi.

Jamilu Gwamna ya yi korafi ga ƴan sanda

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

A baya, an ji cewa dan takarar gwamnan APC a Gombe, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya kai korafi ga Sufeto Janar na 'yan sanda kan zargin bata suna.

Gwamna ya bukaci cibiyar yaki da laifukan intanet ta 'yan sanda tare da hadin gwiwar INTERPOL su binciko masu yada rahoton karya cewa EFCC ta kama shi.

Magoya bayansa sun ce masu adawa sun koma yada karya domin dakile karbuwarsa, yayin da har yanzu 'yan sanda da EFCC ba su fitar da wata sanarwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.