Da Gaske ne Mataimakin Gwamna Ya Ce a Yi wa Tinubu Ruwan Duwatsu?

Da Gaske ne Mataimakin Gwamna Ya Ce a Yi wa Tinubu Ruwan Duwatsu?

  • IbraOfishin Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Ikechukwu Emetu, ya ƙaryata zargin cewa yana ɗaukar samari domin kai wa magoya bayan Shugaba Tinubu da 'yan APC hari
  • Gwamnatin jihar ta kalubalanci kungiyar masoya Tinubu da ta mika kwararan shaidu ko kuma ta tuntuɓi jami'an tsaro domin gudanar da bincike kan zargin
  • Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa yana gudanar da harkokin siyasa ne a cikin lumana da bin doka yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia – Ofishin Mataimakin Gwamnan Abia, Ikechukwu Emetu, ya yi fatali da zargin masoya Shugaba Bola Tinubu na cewa yana shirya samari domin kai wa magoya bayan shugaban kasar da mambobin jam’iyyar APC hari a jihar.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan, Sir Cyril Mba ya fitar, ofishin ya bayyana cewa zargin ƙarya ne, ba shi da tushe ballantana makama, kuma babu hannun Emetu a ciki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya na yi wa 'yan kasa bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bayanin mataimakin gwamna

Vanguard ta rahoto cewa ofishin mataimakin gwamnan ya ƙaryata duk wani zargi na ɗauka, shirya ko ba wa samari makamai domin haifar da rikici.

Sanarwar ta ce:

"Mataimakin Gwamnan ya bayyana ƙarara cewa ba shi da wata alaƙa ko kaɗan wajen ɗaukar samari, haɗa su, ba su makamai ko shirya su domin kai wa magoya bayan Shugaba Tinubu, mambobin APC ko wani mutum ko ƙungiya hari."

An bukaci kawo shaidu

Ofishin mataimakin gwamnan ya ƙalubalanci ƙungiyar masoya Tinubun da kakakin da ya fitar da sanarwar da su fito da shaidar inda aka yi taron ɗaukar samarin, waɗanda suka halarta, da kuma shaidar makaman da ake zargin an rarraba.

Punch ta ruwaito sanarwar tana roƙon rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gayyaci masu zargin domin su bayar da shaidun da suke da su kan wannan al'amari.

Mataimakin gwamnan a shirye yake ya haɗa kai da jami'an tsaro wajen gudanar da bincike na adalci, inda ya bayyana cewa ci gaban da yake samu a fannin siyasa da amincewar da gwamnan jihar, Alex Otti, ya yi masa ne ke sa abokan hamayyarsa fargaba.

Kara karanta wannan

Yadda mutanen Tinubu suka zagaya wajen malaman Izala da Darika a Najeriya

Alex Otti a wajen taro
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti. Hoto: Abia State Government
Source: UGC

Da ake tambayarsa kan matakin da zai ɗauka a gaba, Emetu ya taƙaitawa da cewa:

"Wannan shi ne mafi kyawun abin da zan yi a yanzu."

Sanata Yari ya gana da malamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, yana jagorancin wata babbar tawaga a Najeriya domin neman goyon bayan shugabannin addinin Musulunci.

Tawagar ta gudanar da taruka na sirri a jihohin Plateau, Bauchi, Kaduna, da Kano, inda suka tattauna da manyan malamai da ke wakiltar ɓangarori daban-daban irin su Izala, Tijjaniyya da Qadiriyya.

Sanata Yari yana tare da manyan jigon APC da suka haɗa da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tsofaffin gwamnoni, da kuma mambobin majalisar dokoki domin gudanar da waɗannan tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng