Akwai Kura: Gwamna Ya Yi wa Al’ummarsa Barazana game da Zaben APC a 2027
- Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar hukunta al’ummar Amasiri idan suka ƙi zaɓen APC a babban zaɓen 2027
- Nwifuru ya yi gargaɗin cewa zai ɗauki mataki mafi tsanani kan mutanen idan ya sake samun nasara a zaɓen mai zuwa
- Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da barazanar da Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru a al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya shiga tsakiyar ce-ce-ku-ce bayan zargin yi wa al’ummar Amasiri barazana kan zaɓen da za su yi a 2027.
Amasiri na cikin ƙaramar hukumar Afikpo ta Arewa a Ebonyi, inda gwamnan ya yi gargadin cewa ba zai lamunci al’ummar su zaɓi wata jam’iyya ba.

Source: Twitter
Abin da gwamnan ya ce a bidiyo
A wani bidiyo da ke yawo wanda Amnesty ta wallafa a X, an ji Nwifuru yana gargadin mazauna yankin kan zaɓen jam’iyyar da za su marawa baya.
Gwamnan ya yi magana ne da yaren Igbo, inda ya bayyana cewa zai hukunta mutanen idan suka ƙi zaɓen APC.
Ya ce:
“Idan ba ku zaɓi APC ba, zan hukunta ku. Tabbas zan yi nasara, kuma idan na yi nasarar, zan hukunta ku ta hanya mafi muni.”
Kalaman gwamnan sun jawo damuwa kan yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da barazana da tsoratarwa wajen neman goyon bayan jama’a.
Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da ’yan takara ke ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
A tsarin dimokuraɗiyya, kowane ɗan ƙasa na da 'yancin zaɓen jam’iyyar ko ɗan takarar da yake so ba tare da fuskantar barazana ko tilastawa ba.

Source: Original
Martanin kungiyar Amnesty kan kalaman Nwifuru
Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da barazanar da gwamnan ya yi wa mazauna al’ummar Amasiri da ke ƙaramar hukumar Afikpo ta Arewa, saboda ƙin zaɓen jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnan Edo na da hannu a harin da aka kai wa su Kwankwaso? An samu bayani
Amnesty ta ce babu wani gwamna da ya kamata ya yi wa jama’a barazana saboda sun yi amfani da ’yancinsu na zaɓen wanda suke so.
Ta bukaci rundunar ’Yan Sandan, Hukumar DSS, Hukumar INEC da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Ƙasa (NHRC) su gudanar da bincike kan barazanar tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
"Dole ne Gwamna Nwifuru ya janye kalaman nasa na rashin tunani, sannan ya fito fili ya tabbatar wa mazauna Amasiri cewa za a kare lafiyarsu.
"Wannan ba shi ne karon farko da Gwamna Nwifuru ya yi kalaman barazana ga abokan hamayyarsa na siyasa ba, a ranar 1 ga Satumba, 2026, ya yi gargadin cewa za su fuskanci barazana ta gaske a lokacin da ya dace.”
Gwamna ya sallami wasu jami'an gwamnatinsa
Kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru ya fusata matuka kan mummunan farmakin da aka kai kauyen Okporojo, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen garin Amasiri ne suka kai harin, saboda rikicin da ke tsakaninsu da kauyen Okporojo.
Gwamna Nwifuru ya tsige sarkin yankin tare da korar duk wani dan garin Amasiri da ke rike da mukami a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng
