Nyesom Wike Ya Jero Gwamnonin Jam'iyyar APC 3 da Suka Huro Masa Wutar Adawa
- Nyesom Wike ya bayyana sunayen Hope Uzodimma, AbdulRahman AbdulRazaq da Dapo Abiodun cikin masu adawa da shi
- A cewar Ministan Abuja, gwamnonin sun yi kokarin ganin mutanensu sun samu tutar APC saboda lissafin shugabancin majalisa
- Wike ya yi zargin cewa muradun gwamnonin sun sa da yawa daga cikin 'yan APC da aka hana tikiti sun zo wajensu a PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan harkokin birnin Abuja, Mista Nyesom Wike ya ambaci wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ya ce suna yaki da shi.
Nyesom Wike ya kafa gangamin Rainbow Coalition Movement wadanda gwamnonin APC suke ganin cewa barazana ce a 2027.

Source: Facebook
Mai girma ministan ya bayyana wannan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a yammacin ranar Litinin.
Rainbow Coalition Movement wani gamin-gambiza ne na ‘yan siyasa daga jam’iyyu dabam-dabam da ke tare da Bola Tinubu.
Gwamnoni 3 da ke fada da Nyesom Wike
A hirar da aka yi da shi, Nyesom Wike ya ce daga cikin masu yakar wannan tafiya ta shi akwai Sanata Hope Uzodimma na Imo.
Ya kuma ce akwai shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq da Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.
Premium Times ta rahoto Wike ya ce son kai kawai ya jawo gwamnonin suke fada da shi.
Ministan ya ce gwamnonin APC da suka biye wa PGF ba su da dalilin yin haka domin ba su da irin matsalar wadancan su ukun.
Tsoron da gwamnonin APC ke yi wa Wike
Wike yake cewa Hope Uzodimma, AbdulRazaq da Dapo Abiodun sun dage cewa PDP ba za ta samu ‘yan takara a jihohinsu ba.
Tsohon gwamnan Rivers ya ce tsoron gwamnonin shi ne ‘yan takaran APC a zaben sanata da majalisun dokoki ba su yi nasara ba.
Ya kuma ce gwamnonin na dar-dar cewa masu neman takaran da suka bar APC kuma suka samu tikiti a PDP za su iya yakar Tinubu.
"Mutanen nan sun zo neman mafaka a PDP, wanda ta ke goyon bayan Tinubu sai kuma ku gwamnonin nan ku yi fushi.
"Da sun shiga ADC ko NDC - su da ke adawa da Mai girma shugaban kasa - abin da suke so kenan?"
- Nyesom Wike
A tattaunawar, Wike ya ce gwamnonin sun ba mutanensu tikitin APC saboda su shirya wadanda za su shugabanci majalisar tarayya.
Sai dai a kokarin yin hakan, jagoran na PDP ya yi ikirarin gwamnonin APC sun haifar da rikicin gidan da zai iya cin su a zaben 2027.
Mista Wike ya dage cewa Mai girma shugaban kasa ya san abubuwan da yake kitsawa, abin da ya hada shi fada da wasu 'yan PGF.
Bangaren hirar da aka yi da Wike kamar yadda shafin Nig Affairs ya wallafa a X.
Wike ba zai goyi bayan Uzodinma ba
Labarin nan cewa yake yi Ministan Abuja, Nyesom Wike ba zai taba goyon bayan burin Gwamna Hope Uzodimma na zama Shugaban Majalisar Dattawa ba.
Wike ya zargi Uzodimma da wasu gwamnonin APC da kokarin yin amfani da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar wajen sanya mutanensu a Majalisar Tarayya.
Ministan ya ce "Rainbow Coalition" da yake jagoranta ba ta nufin yi wa jam'iyyar APC zagon kasa ba ne, illa taimakon Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Asali: Legit.ng


