El Rufai: Limami Ya Aika wa Uba Sani Sako a Mimbarin Juma’a, Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Fada
- Sanusi Khalil bai goyon kama Nasir El-Rufai da aka yi aka rufe ba tare da an kai ga yi masa hukunci ba
- Malamin addinin ya kawo maganar tsohon gwamnan a wata hudubar Juma’a da ake zargin ya yi kwanan nan
- Sheikh Sanusi Khalil ya tuna wa Uba Sani rawar da El-Rufai ya taka wajen ganin ya zama gwamnan Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Shehin malamin Musulunci, Sunusi Khalil, ya bukaci a yi wa Nasir El-Rufai yayin da ake cigaba da tsare shi.
Sunusi Khalil ya yi maganar lamarin tsohon gwamnan Kaduna a hudubar ranar Juma’a, 7 ga watan Rabiu Thani 1448.

Source: Facebook
Sanusi Khalil ya yi magana kan Nasir El-Rufai
Legit Hausa ta ci karo da hudubar malamin waken Bashir Garba Sufyan a kafar X, inda ya fara da kiran gwamna da ‘danuwa.
Babban malamin yana ganin babu adalci a ce ana ta rike Nasir El-Rufa’i duk da cewa kotu ba ta same shi da aikata laifi ba.
A hudubar da ya yi, Sheikh Sunusi Khalil ya ce ya kamata duk wanda ake zargi da laifi, a kai shi kotu domin a yi masa hukunci.
Duk tsawon hukunci, shehin malamin addinin Musuluncin ya ce gara a yanke wa mutum domin ya san wata rana zai iya fito wa.
Akwai wadanda ya ce aka yanke wa daurin shekaru 70, idan da kwana gaba, limamin ya ce zai fito.
Matsayin da Uba Sani a mulkin El-Rufai
Daily Post ta rahoto shi yana tuna wa Gwamna Uba Sani irin abubuwan da ya fada, ya kira Malam El-Rufai da uba da bakinsa.
Malamin ya soma da tuna wa Mai girma Uba Sani yadda ya tashi a unguwar Tudun Wada, har ya samu a fada a gwamnatin baya.

Kara karanta wannan
Sarki Bamalli ya karyata cewa alakar jini ta jawo El Rufai ya nada shi Sarkin Zazzau
Yake cewa El-Rufai ya goyi bayan Uba Sani ya zama gwamna kuma ya ba shi damar da bai ba sauran masu ba da shawara ba.
A wa’azin ne ya dauko labarin yadda aka rika kiran Uba Sani da ka-fi-gwamna tun lokacin bai zama sanata a majalisar dattawa ba.
Gwamnan Kaduna yake da hannu a tsare El-Rufai?
Ko da akwai wani sabani a tsakaninsu, ya roki shugaban ya bari a yi wa tsohon gwamnan adalci.
Hudubar ta kuma tuna yadda wasu kungiyoyin Arewa da na Musulmai suka ja hankalin Bola Tinubu game da batun tsare El-Rufai.
A cewar malamin, shugaban kasa ya ce babu hannunsa, ya bukaci masu neman a saki ‘dan siyasar da su yi magana da gwamna Uba.
Sheikh Sanusi Khalil ya ce:
“Omo Logo ya bude baki ya ce a’a, shi fa babu hannun shi a wajen rike Nasiru. Ku koma wajen gwamna ku yi magana da shi.”
Bayan haka, hudubar Juma’ar malamin ta yi wa gwamnan jihar Kaduna wa’azi cewa idan zai gina ramin muguna, ya gina shi gare.
Rikicin Wike da gwamnonin APC
An ji labarin yadda tazarce, neman fada wajen Bola Tinubu da wasu abubuwa suka zama silar rikicin gwamnonin APC da Nyesom Wike.
Ban da tarayyarsu ta goyon bayan Bola Tinubu na 2027, akwai sabani birjik tsakanin gwamnonin APC da Ministan da ke kula da Abuja.
Sabanin Nyesom Wike ta fito bainar nasi kwanan nan da gwamnonin suka nuna cewa babu ruwansu da wasu kungiyoyin da ke wajen APC.
Asali: Legit.ng

