An Fara Maganar Shugaba Tinubu Ya Shekara 10 a kan Mulki
- Tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, ya ce ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da mulki na wasu shekaru 10 idan hakan zai yiwu
- Akande ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da gyare-gyaren da Tinubu ke aiwatarwa za su kawo sauyi mai dorewa idan aka ba shi karin lokaci
- Tsohon gwamnan kuma jagora a jam'iyyar APC ya kuma zargi gwamnatocin mulkin soja da raunana noma, ilimi da tattalin arzikin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, ya bukaci a bar Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da mulki domin kammala ayyukan raya kasa da gyare-gyaren da ya fara.
Ya ce Najeriya na bukatar shugabanci mai dorewa domin shawo kan matsalolin da suka samo asali daga tsawon shekarun mulkin soja.

Kara karanta wannan
Tinubu Ya Tuna da Iyalan Sojojin da Suka Mutu a Hatsarin Jirgi, Ya ba Su Abin Duniya

Source: Facebook
Puch ta wallafa cewa Akande ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin da aka wallafa a ranar Juma’a.
Akande na si Tinubu kara wa’adi
Da yake bayyana dalilin da ya sa yake son Tinubu ya ci gaba da mulki, Akande ya ce ya kamata shugaban kasar ya samu damar kammala ayyukan da ya fara.
Ya yi nuni da kalaman Olubadan kan ayyukan tituna da ake gudanarwa a Kudu maso Yamma, musamman hanyoyin da suka hada Ijebu-Ode, Abeokuta, Oyo da Ikire.
A cewarsa, Olubadan ya nuna cewa idan ana gudanar da irin wadannan ayyuka da ba a taba yi ba tsawon shekaru 50, to ya kamata a ba shugaban kasar damar kammala su.
Akande ya ce:
"Me kuma kuke so in fada? Ya kamata a bar Bola Tinubu ya yi wasu shekaru hudu domin ya kammala kyakkyawan aikin da ya fara.
"Idan zai yiwu, ya kamata ya ci gaba da zama a ofis na wasu shekaru 10, in ba haka ba za mu koma halin da ake ciki na Ebinpawa, domin an riga an kafa tubalin yunwa."

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Akande ya caccaki mulkin soja
Tsohon gwamnan ya dora alhakin tabarbarewar noma, ilimi da ci gaban tattalin arzikin Najeriya kan gwamnatocin soja da suka jagoranci kasar a baya.
Ya ce tun bayan fara mulkin soja a shekarar 1966, an yi watsi da noma, ayyukan yi da ilimi, lamarin da ya haifar da matsalolin da kasar ke fuskanta.
Akande ya ce:
"Shekaru 40 kafin zuwansa, tun daga 1966 lokacin da sojoji suka fara mulkinku, kuna gina tubalin yunwa. Kun yi watsi da gonakinku, kun yi watsi da aiki, kun ki samun ilimi kuma kun ki zamanantar da kanku."

Source: Twitter
Ya kuma bayyana fatansa cewa nan da shekaru 10, gyare-gyaren Tinubu za su samar da wutar lantarki a ko'ina tare da kawo zamanantar da kasar.
An nemi Obi ya janye takara
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Hukumar Bincike da Bunƙasa Albarkatun Ƙasa (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ike-Muonso, ya bukaci Peter Obi ya janye takararsa ta shugaban kasa a zaben 2027.
Ike-Muonso ya kuma bukaci ’yan Najeriya su goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu domin ya samu damar ci gaba da aiwatar da manufofinsa na tattalin arziki.
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar ya ce ya kamata Kudancin Najeriya ya kammala wa’adin mulkin shekara takwas kafin a mayar da mulki zuwa Arewa.
Asali: Legit.ng
