Tsohon Kwamishina Ya Tsoma Ganduje da Abba ke ‘Karar’ Kwankwaso ga EFCC
- Tsohon kwamishinan Kano ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da nuna rashin adalci kan kai karar Rabiu Kwankwaso ga EFCC
- Mu’azu Magaji ya ce bai kare Kwankwaso daga duk wani zargin rashawa ba ne, sai dai yana tambayar dalilin da ya sa gwamnati ke mayar da hankali kansa
- Gwamnatin Kano ta musanta hannu a binciken Kwankwaso, tana mai cewa alakarsa da hukumar ta fara ne tun kafin gwamnatin Abba Yusuf ta hau mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon kwamishinan ayyuka da gine-gine na Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya zargi gwamnatin jihar Kano da butulci.
Magaji ya ce gwamnatin ta nuna rashin adalci da rashin godiya ga Rabiu Musa Kwankwaso wurin tura shi ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma'a, tsohon kwamishinan ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin rashin godiya da rashin adalci.
Magaji ya soki gwamnatin Abba Kabir
Magaji, wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, ya tambayi dalilin da ya sa gwamnatin ke mayar da hankali kan Kwankwaso, yayin da ta kasa daukar mataki kan zarge-zargen rashawa da ake dangantawa da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin Kano ta tsallake Ganduje ta kai karar Kwankwaso ga EFCC kan zargin rashawa.
Magaji, wanda ya rike mukamin kwamishina a gwamnatin Ganduje, ya bayyana cewa kalamansa ba wai kare Kwankwaso daga duk wani zargi ba ne, sai dai yana nuna damuwa kan yadda ake kallon zarge-zargen rashawa na tsoffin shugabanni ta hanyoyi daban-daban.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da takaddama ke kara kamari tsakanin Kwankwaso da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin binciken da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan.

Source: Facebook
Zargin da Kwankwaso ke yi wa Abba
A baya, Kwankwaso ya zargi gwamnatin jihar da amfani da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa wajen bata masa suna da kuma raunana karfinsa na siyasa gabanin babban zaben 2027.
Sai dai gwamnatin Kano, ta bakin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta musanta zargin, tana mai cewa Gwamna Abba Yusuf ba shi da hannu a al'amuran Kwankwaso da EFCC.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa alakarta da hukumar EFCC kan Kwankwaso ta samo asali ne tun kafin gwamnatin yanzu ta hau mulki.
Takaddamar ta kuma sake dawo da batun zarge-zargen da suka shafi mulkin Ganduje, musamman bidiyon dala da ya yadu a kafafen sada zumunta da sauran batutuwan da suka shafi kudade da har yanzu ake ta muhawara a kansu.
Wannan takaddama na zuwa ne yayin da sabani da sauye-sauyen kawancen siyasa ke ci gaba da tasiri a siyasar Kano gabanin babban zaben 2027.
Abba zai kawo karshen tsadar haya
A baya, an ji cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirin kafa hukumar kula da harkokin gidaje domin dakile tashin gwauron zabin kuɗin haya da sauran matsaloli a ɓangaren gidaje.
Kwamishinan gidaje na jihar, Ibrahim Yakubu-Adamu, ya ce tuni aka aika da takardar neman amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafa hukumar.
Ya bayyana cewa hukumar za ta sa ido kan masu harkar gidaje tare da magance abubuwan da ke haddasa tsadar haya a jihar Kano baki daya.
Asali: Legit.ng


