Rashin Imani: Yan Bindiga Sun Tashi Gari, Sun Banka Wa Gidaje da Shaguna Wuta
- Mahara da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari Lumma Sanke da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja, inda suka ƙona gidaje, shaguna da sauran kadarori
- Rahotanni sun ce iyalai da dama, ciki har da mata da yara, sun tsere daga gidajensu bayan maharan sun cinnawa kadarorinsu wuta
- Wannan harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan kashe mutane da dama, ciki har da dagacin Lumma Ba’are, Mallam Bawa Muhammad, a wani hari da aka kai ranar 21 ga Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga sun kai hari garin Lumma Sanke da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.
A yayin harin, an ruwaito cewa maharan da ke dauke da makamai sun ƙona gidaje, shaguna da sauran kadarori, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin da dama barin gidajensu.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun tarfa mutanen gari da daddare, sun kashe mata, yara da matasa da dama

Source: Original
Mahara sun tarwatsa mutanen gari
Rahotanni da jaridar Leadership ta tattaro sun ce harin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, 2026.
Bayanan da mazauna yankin suka bayar da bidiyoyin da ke yawo daga wurin sun nuna cewa maharan sun kai hari kan al'ummar Kambari.
An ce iyalai da dama, ciki har da mata da yara, sun tsere daga gidajensu bayan yan bindigar sun ƙona kadarorinsu, lamarin da ya bar mutane da dama cikin halin gudun hijira.
Hari na biyu cikin kwanaki
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani mummunan hari da aka kai makwabciyar al’ummar Lumma Ba’are a ranar 21 ga Nuwamba, 2026.
A yayin harin, an ruwaito cewa an kashe mazauna yankin da dama, ciki har da dagacin garin, Mallam Bawa Muhammad.
Sabon harin ya ƙara tayar da hankula kan matsalar tsaro da ke addabar al’ummomin yankin Borgu, inda mazauna yankin ke kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki.
Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Neja ko wasu hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwar hukuma kan sabon harin ba.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
