Sanata Shehu Sani Ya Cire Atiku cikin Wadanda Ya Kamata Su Nemi Shugaban Kasa

Sanata Shehu Sani Ya Cire Atiku cikin Wadanda Ya Kamata Su Nemi Shugaban Kasa

  • Kwamred Shehu Sani bai ganin dacewar wani daga Arewa ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027
  • Ya bukaci a bar Bola Tinubu ya gwabza da irinsu Peter Obi, Yele Sowore, Donald Duke da su Seyi Makinde
  • Tsohon Sanatan na Kaduna yana ganin sai a 2031 sannan ya dace a samu ’yan takara daga yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya sake tada kura da rubutun da ya yi game da takarar shugaban kasa.

Shehu Sani ya ce zaben shugaban ƙasa na 2027 ya kamata ya kasance tsakanin ’yan takarar da suka fito daga Kudancin Najeriya.

Bola Tinubu da Shehu Sani
Sanata Shehu Sani da Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: Reno Omokri Shehu Sani
Source: Facebook

Shehu Sani ya kore takarar 'yan Arewa

Kwamred Shehu Sani ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya yi hasashen makomar Tinubu da kuri'un da APC za ta samu

A nan ya yi magana kan batun kama-kama da ake yi da mulki tsakanin yankin Arewa da Kudu da kuma makomar siyasar Najeriya.

Tun da yanzu mulki yana hannun mutumin Kudu, Shehu Sani bai goyon bayan a ce an samu wani daga Arewa da zai kalubalance shi.

Kwamred Sani wanda a da yake adawa ya rubuta cewa bai kamata a yi watsi da tsarin ba duk da bai cikin kundin tsarin mulkin kasa.

Su wa ya dace su tunkari Bola Tinubu?

Kuma ya ce cikin ’yan siyasar da ya kamata su fafata da Shugaba Bola Tinubu akwai Peter Obi, Omoyele Sowore da Adewole Adebayo.

Tsohon ‘dan gwawarmayar wanda yanzu yake takarar sanata ya bude kofar ga Seyi Makinde da kuma tsohon gwamna Donald Duke.

Kara karanta wannan

Wasu matasa da aka sa a kwamitin yakin zabe sun wulakanta Tinubu a gaban kowa

A cewarsa, ya kamata Kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas na shugabanci kafin a mayar da mulki Arewa nan da shekaru hudu.

Ya ja hankali cewa idan aka yi watsi da tsarin karba-karba wajen mulkin a 2027, mutanen Kudu za su sake tsaya wa takara a 2031.

“Ya kamata takarar 2027 ta kasance tsakanin Tinubu, Peter Obi, Sowore, Makinde, Adebayo, Duke da sauran ‘yan takaran Kudu.
"Yankin Kudu ya kammala shekarunsa takwas. Ba dokar kasa ba ce, amma adalci ne.
"A kyale ‘yan Arewa su tsaya takara babu hamayya a 2031. masu cewa a yi watsi da tsarin karba-karba a 2027, su sani cewa ba za a yi amfani da shi a 2031 ba."

- Shehu Sani

Sai dai bai yi maganar abin da zai faru idan wani ‘dan Kudu ya ci zabe a 2027 ba, hakan zai iya ba yankin damar yin shekaru 12.

Sanatan APC zai yi doya da manja a 2027?

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai ragargaji Atiku da Tinubu a zaben 2027 a Kano

An ji cewa Sanata Bala Na’Allah wanda ‘dan APC ne, ba zai damu kan shi ba, zai goyi bayan jam’iyyar da al’ummarsa ke so a zaben 2027.

Tsohon sanatan na Kebbi ya bayyana cewa har yanzu yana nan a APC ba zai tilasta wa mutanensa zabin jam'iyyar da ba su so ba.

Ya jaddada cewa a zaben 2027 mai zuwa, zai goyi bayan duk jam'iyyar da al'amarinta ya fi kwanta wa jama'arsa na kudancin Kebbi a rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng