Yaudara Babu Kyau: Shehu Sani ya Kalubalanci APC a Tikitin Musulmi da Musulmi

Yaudara Babu Kyau: Shehu Sani ya Kalubalanci APC a Tikitin Musulmi da Musulmi

  • Shehu Sani ya caccaki mutanen da ya ce su na yaudarar al’ummar jihar Kaduna da addini a siyasa
  • Tsohon ‘dan majalisar ya zubo irin alheran da ya yi wa Musulmai a lokacin da yake rike da kujera
  • Sanata Shehu Sani yana so ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su fadi irin guudmuwar da suka ba Musulunci

Kaduna - Shehu Sani ya fito yana shagube a game da yadda wasu suke kokarin cefanar da addini domin tallata ‘dan takaransu a zaben jihar Kaduna.

Sanata Shehu Sani ya yi magana a dandalin Facebook, ya lissafo yadda ya taimakawa addinin Musulunci a lokacin da ya yi aiki a majalisar dattawa.

‘Dan gwagwarmayar ya shaida cewa a sa’ilin da yake rike da kujerar Sanata, ya tanadi gidajen marayu a Kaduna domin taimakawa ‘ya ‘yan musulmai.

Kara karanta wannan

Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

Shehu Sani yake cewa ya samu damar taimakawa da makarantun Islamiyya da kuma ginawa Musulmai masallatai domin al’umma su ji dadin ibada.

Irin kokarin Shehu Sani

Legit.ng Hausa ta bibiyi shafin tsohon ‘Dan majalisar, ta ji yana bayanin yadda ya tallafawa kungiyoyin Izala da na Darika tsakanin 2015 zuwa 2019.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karshe Kwamred Sani ya jefa kalubale wanda zai tafi ga jam’iyyar APC da magoya bayansu, yana cewa su lissafo gudumuwar da suka ba musulunci.

Shehu Sani
Shehu Sani a filin idi Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Babu mamaki tsohon ‘dan takaran Gwamnan a PDP ya dauko wannan magana ne ganin yadda ake magana a kan tikitin Uba Sani da Dr. Hadiza Balarabe.

Maganar da Kwamred ya yi a Facebook

“Mun sayi gida guda biyu na marayun musulmi a Giwa da Birnin Gwari.
Mun sayi gida guda biyu a Ungwan Shanu da Tudun Nupawa muka ba kungiyan Izala ana Islamiya a cikin su.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi

Mun Gina massalaci a Jere.
Mun sayi gida, mu ka ba yan Darikar Tijjaniya a Rigasa dan su mai dashi asibiti.
Mun bada gudun mawan masallatai ga kungiyan Izala da darika.
Duka a je a binciki wannan magana.
'Yan Siyasan Kaduna masu Muslim Muslim ticket su fadi abun da suka yi ma musulunci ban da gina manyan gidaje na su da iyalan su.
Yaudara da amfani da addini bai yi ba wolla.
Mu ga namu kowa ya fadi nashi..ehe."

- Shehu Sani

Ana cafke 'Yan PDP

A wani rahoto na dabam, an ji jami'an tsaro sun yi ram da Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Kaduna a makon nan.

Ahmed Muhammad Makarfi ya fitar da jawabi cewa akwai jagororin PDP da ake harin cafkewa a yankunan Kudan, Sanga, Igabi, Lere, Kachia da Jaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel