Ina Nan a APC amma Zan Goyi Bayan Jam’iyyar da Mutane Suke So In ji Sanata Na’Allah
- Bala Ibn Na’Allah ba zai taba tilasta wa mutanensa goyon bayan jam’iyyar da ba su so ba a zaben 2027
- Tsohon sanatan yana nan a jam'iyyar APC, sai dai yana ta nazarin abubuwan da za su yi faruwa kafin zabe
- Na’Allah ya janye daga zaben fitar da gwani na APC a baya, ya yi zargi cewa an riga an tsara wanda ake so
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kebbi - Bala Ibn Na’Allah ya ce har gobe yana nan a jam’iyyar APC duk da bai rike da wani babban mukami a siyasa a yau.
Tsohon ‘dan majalisar dattawan ya ce kasancewarsa a APC, ba zai hana mutanensa su zabi jam’iyyar da suka ga dama ba.

Source: UGC
Bala Ibn Na'Allah zai yi wa APC kamfe?
A zantawarsa da tashar Arise, Sanata Bala Ibn Na’Allah ya nuna zai goyi bayan duk jam’iyyar da jama’ansa suka zaba.
A zaben tsaida gwani na APC, tsohon sanatan ya janye daga takarar neman tikitin majalisa, yana kukan rashin adalci.
Bayan fushin da ya yi da jam’iyyarsu ta APC mai mulki, an tambaye shi ko yana tare da ita a babban zaben shekarar 2027.
A matsayinsa na wanda ya san dimukaradiyya, Ibn Na’Allah ya ce goyon bayansa tana ga duk abin da talakawansa suke so.
Muradin jama'an Kudancin Kebbi shi ne nasa
A takarar 2027, Sanata Ibn Na’Allah ya ce ba zai yi amfani da matsayinsa, ya tursasa a jama’a su zabi wanda ba shi suke so ba.
Ya ce:
"Bari in fada maka gaskiya. Ina jam’iyyar APC. Amma idan wani dalili ya sa mutanena suna ganin ba APC ce jam’iyyar da suke so ba. Matsayina a siyasa bai kai ni inda zan fada wa mutane su yi abin da ba su zo.
"Na yi amanna da abin da mutanena suke so."

Kara karanta wannan
‘Yan Boko Haram sun yi sabon bidiyo da ya yi maganar batun sulhu da Gwamnatin Tarayya
Vanguard ta rahoto shi yana cewa yana nazarin yadda abubuwa suke tafiya ganain zabe, ya ce suna daukar darasin siyasa a kullum.
Sanata Na'Allah ya fi karfin wulakanci a siyasa
A hirar, ya bayyana cewa a matakin da ya rike na Mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawa, ya fi karfin ya tozarta.
‘Dan siyasar ba zai taka wadannan matsayi ba, sai kuma a yau ya koma yana rike wa minista takardu, ya ce babu cigaba a nan.
Kasancewarsa ‘dan kasuwa, lauya kuma matukin jirgin sama da ‘ya ‘ya uku kadai ya haifa, bai ga dalilin wulakanta kan shi ba.
Ibn Na’Allah ya ce yara biyu suka rage masa a raye kuma duk sun girma suna tukin jirgi, su kansu za su iya kula da shi a duniya.
Imran Muhammad ya wallafa bangaren hirar ta ranar Litinin a shafin Facebook.
Mutanen Buhari masu yakar Tinubu a 2027
Kun ji labari wasu wadanda aka yi gwamnatin Muhammadu Buhari suna kalubalantar tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
An sake rusa lissafin Tinubu, tsohon shugaban Majalisar dokoki ya fice daga jam'iyyar APC
Irinsu Rotimi Chibuike Amaechi da Lawal Daura suna cikin tikitin 2027, suna neman zama mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyun adawa.
Shi Rt Hon Chibuike R Amaechi ya yi minista yayin da Lawal Musa Daura ya dawo ya rike hukumar DSS.
Asali: Legit.ng
