PDP Ta Yi Magana kan Batun Hada Kai da Su Atiku a Kayar da Tinubu
- Jam’iyyar PDP da ke biyayya ga Nyesom Wike ta ce ba ta cikin ƙungiyar haɗakar jam’iyyun siyasa da ake kira Coalition for Democracy
- PDP ta bayyana cewa ba za ta halarci taron haɗakar da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Nuwamba na shekarar 2026 ba
- Jam’iyyar ta kuma yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin shari’a kan duk wanda ya ci gaba da amfani da sunanta ba tare da izini ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar PDP mai biyayya ga jagoran ta, Nyesom Wike, ta nesanta kanta da shirin haɗakar jam’iyyun siyasa da ake kira Coalition for Democracy, wanda Salihu M. Lukman ke jagoranta.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Hon. Jungudo Haruna Mohammed, ya fitar a ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026, PDP ta ce ba ta amince da shiga ƙungiyar ko halartar taron da aka shirya yi a ranar 30 ga watan ba.

Source: Facebook
A sakon da Jungudo ya wallafa a Facebook, jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa wasu tsoffin mambobinta da aka kora ne ke ikirarin wakiltarta a wannan shiri, duk da cewa kotuna sun yi watsi da ikirarinsu.
PDP ta ce ba ta cikin haɗakar
A sanarwar, PDP ta ce ba ta cikin ƙungiyar Coalition for Democracy, kuma ba ta ba kowane mutum ko wata ƙungiya izinin wakiltarta a taron da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Nuwamba.
Ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani mataki ko matsaya da za a ɗauka a madadin jam’iyyar a wannan taro ba.
PDP ta kuma buƙaci jama’a da kafofin watsa labarai su yi watsi da rahotannin da ke danganta ta da taron ko wata yarjejeniya ta siyasa da Salihu Lukman da abokan hulɗarsa ke shiryawa.
PDP ta yi bata mata suna
PDP ta ce mutanen da ake gabatarwa a matsayin wakilanta tsoffin mambobi ne da aka kora daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan
An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana
A cewar sanarwar, ikirarin mutanen na jagoranci da wakiltar PDP ya sha fuskantar rashin nasara a Kotun Tarayya, Kotun Ɗaukaka Ƙara da kuma Kotun Ƙoli.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa kotuna sun hana Kabiru Tanimu Turaki SAN da abokan tafiyarsa gabatar da kansu a matsayin shugabannin PDP.
Haɗakar da PDP ta amince da ita
Jam’iyyar ta yi kira ga Salihu Lukman da abokan hulɗarsa da su daina amfani da sunanta, tambarinta da ikonta na hukuma wajen gudanar da ayyukansu na siyasa.
Ta ce za ta iya ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda ya ci gaba da danganta ta da wannan haɗaka ba tare da izini ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa Rainbow Coalition ce kaɗai haɗakar siyasa da PDP ta bayyana aniyarta ta shiga, bisa umarni da jagorancin Nyesom Wike.

Source: Facebook
PDP ta ce ba za a amince da wani shiri na daban a matsayin matsayinta na hukuma ba, tare da jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da sunanta wajen cimma muradun wasu mutane ba.
PDP ta yi wa APC jaje a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa tawagar PDP ƙarƙashin jagorancin Dan’azumi Adamu Pindiga ta ziyarci shugabannin APC da suka jikkata a wani hatsarin mota a jihar Gombe.
Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na jihar, Sa’adu Hassan, da shugaban jam’iyyar, Dantata Ndus.
PDP ta bayyana cewa bambancin jam’iyya bai kamata ya hana ’yan siyasa nuna tausayi, zumunci da mutunta juna ba, musamman idan wani ya shiga cikin mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng

