Malamin Musulunci Ya Sha Kaye a Kokarinsa na Samun Tikitin Takarar Gwamnan Kano a 2027

Malamin Musulunci Ya Sha Kaye a Kokarinsa na Samun Tikitin Takarar Gwamnan Kano a 2027

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sha kashi a ƙoƙarinsa na zama halastaccen dan takarar gwamna a ADC
  • Mai shari’a SM Shuaibu ya yi watsi da ƙarar malamin a ranar Litinin, yana mai cewa bai gabatar da isasshiyar hujjar cewa ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ba
  • Kotun ta ce hukumar INEC ba ta sa ido kan zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar a ranar 22 ga Mayu, 2026, kamar yadda doka ta tanada ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban Majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi rashin nasara a karar da ya shigar kotu.

Malamin ya sha kashi a ƙoƙarinsa na maye gurbin Alhaji Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Little, a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a jihar Kano a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Amaechi ya jero jihohin ya ce tabbas Atiku zai lashe su a 2027

Ibrahim Khalil.
Babban malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khali Hoto: Sheikh Ibrahim Khalil
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa a yau Litinin, Mai shari’a SM Shuaibu ya yi watsi da ƙarar da malamin ya shigar, inda yake neman a maye gurbin Ali Amin da shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar.

Kotu ta kori karar Ibrahim Khalil

Alƙalin ya bayyana cewa hujjojin da mai ƙara ya gabatar ba su isa su tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwanin ADC da aka gudanar a watan Mayu ba, wanda ya kamata a ce hukumar INEC ta sa ido a kai.

“Mai ƙara ya kasa tabbatar da cewa INEC ta sa ido kan zaɓen fidda gwanin da kafa hujja da shi kamar yadda doka ta tanada.
“Ba a gayyaci INEC ba, kuma ba ta sa ido kan zaɓen fda aka gudanar a ranar 22 ga Mayu, 2026, domin samar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, sabanin abin da mai ƙara ya yi iƙirari,” in ji alƙalin.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fito ya gayawa duniya wani halin Peter Obi

Mai shari’a Shuaibu ya ce sashe na 29(1) na dokar zaɓe ya tanadi cewa kowace jam’iyyar siyasa dole ne ta miƙa wa INEC sunayen ’yan takararta da suka fito daga zaɓen fitar da gwani wanda hukumar ta sa ido a kai.

Kotun ta amince da haƙƙin malamin

Tun da farko, alƙalin ya amince da haƙƙin malamin na shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya kan zargin rashin bin ƙa’ida yayin zaɓen ’yan takara, kamar yadda aka tanada a sashe na 88.

Ya bayyana cewa babu wata doka da za ta hana ɗan jam’iyya da ya ji an zalunce shi neman haƙƙinsa a kotu.

ADC .
Tambarin jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Kotun ta amince d ƙalubalen farko da Ibrahim Little ya shigar, inda ya yi iƙirarin cewa wa’adin shigar da ƙarar ya wuce saboda an shigar da ita bayan kwanaki 14 da doka ta tanada.

Saboda haka, ya ce a mahangar doka, an kawo karar ne a watan Agusta, lokacin INEC ta karɓi sunan Little, ba a watan Satumba ba, lokacin da mai ƙara ya samu labarin miƙa sunan ba.

Dalilin INEC na cire sunan Aminu Gwarzo

Kun ji cewa takardun kotu sun tabbatar da cewa INEC ta hana wallafa sunan Aminu Gwarzo bisa umarnin wucin gadi na Babbar Kotun Tarayya.

Mambobin NDC uku ne suka shigar da ƙara kan yadda aka zaɓi Gwarzo da abokin takararsa, Mustapha Rabiu Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262