Wasu Matasa da Aka Sa a Kwamitin Yakin Zabe Sun Wulakanta Tinubu a gaban Kowa
- Muhammad Murtala Musa D Provost ya ki karbar tallar APC a 2027, ya ce su ke da alhakin halin ƙuncin da ’yan Najeriya ke ciki a yau
- Matashin zai mayar da hankalinsa wajen tallar duk wani ɗan takara da ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya yi nasara
- Shi ma Abubakar Gossima ya ce babu abin da ya hada shi da tallata Shugaban kasa Tinubu a shekarar 2027, domin ya bi layin ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar APC ta fitar da jerin mutanen da za su taya ta aikin tallata Bola Tinubu da Kashim Shettima a zabe mai zuwa a 2027.
Sai dai wasu daga cikin wadanda aka sa sunayensu a kwamitin yakin neman zaben sun barranta, sun ce babu ruwansu da APC.

Kara karanta wannan
Abdulaziz Yari ya fadi sirri da ya kama aikin tallar Tinubu babu kama hannun yaro

Source: UGC
2027: D Provost ya ki karbar aikin tallata APC
Muhammad Murtala Musa D Provost na cikin matasan da suka watsa wa APC kasa a ido a sahar Facebook, suka ce ba za su tallata su ba.
Tun a farkon makon nan Murtala Musa D Provost ya fito ya sanar da duniya cewa yana tare da wanda yadawo da tallafin man fetur.
Yake cewa ya samu labarin an fitar da jerin ‘yan kwamitin harkokin sadarwa na zamani da su yi wa APC kamfen a babban zabe.
A ciki sai aka sa sunan shi, suna karkashin hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun, shi kuwa ya fada wa duniya bai karbi aikin ba.
Lauretta Onochie a X ta rahoto Murtala Musa D Provost ya ce a zabe mai zuwa, ba zai kare gwamnatin da ta jefa talakawa a masifa ba.
Matashin ba zai yi wa jam'iyyar APC kamfe ba
Murtala Musa D Provost ya fadin zabinsa, ya ce:

Kara karanta wannan
Hankalin Dangote ya tashi kan maido tallafin mai, Atiku ya masa bayani dalla dalla
“Zan yi amfani da karfi na wajen tallata wanda ya yi alkawarin maido tallafin fetur idan ya ci zaben shugaban kasa.
“Ina nanata cewa na yi watsi da wannan naɗi baki ɗaya, kuma na ƙi amincewa da shi saboda wannan dalili”
Abubakar Gossima ya koma jam'iyyar ADC
Haka zancen yake wajen Abubakar Gossima wanda shi ma sunansa yana cikin ‘yan kwamitin kamfen APC a takarar shugaban kasa.
Ya yi godiya, amma ya tabbatar da ba zai yi wa Bola Tinubu kamfe ba domin a yanzu shi ‘dan ADC ne da yake tare da Atiku Abubakar.
Malam Abubakar Gossima ya sanar da kin karbar aikin yakin zaben a shafin Facebook.
Jawabin kin karbar aikin taya APC kamfe
Ya rubuta:
"Ina matuƙar godiya da wannan karamci da kuma yadda da yin la’akari da ƙoƙari na da amincewa da ni. Duk da haka, bayan nazari da tunani mai zurfi, na yanke shawarar ƙin karɓar wannan naɗi, saboda wasu dalilai da suka shafi cigaban ƙasar mu Nigeria...
"Wannan ba yana nufin na ƙi girmamawa ko amincewar da aka nuna min ba. A'A Ina matuƙar daraja wannan dama kuma ina roƙon Allah Ya saka da alheri, Ya kuma ba mu damar ci gaba da yi wa al’umma hidima ta hanyoyin da suka dace.
"Na gode ƙwarai da wannan amana da damar da aka ba ni. Allah Ya saka da alheri...
"Yanzu ni Abubakar Gossima ɗan jam'iyyar ADC ne kuma dan takarar ta Atiku Abubakar da sauran yan takarkaru na cikin jam'iyyar na aminta na yiwa aiki domin ganin nasarar su a zaɓen 2027 me zuwa...
Nagode..."
Tinubu: Abdulaziz Yari ya soma aikin kamfe
An ji Abdulaziz Yari ya yanke shawarar fara yakin neman zaben daga mahaifarsa ta jihar Zamfara kafin ya gudanar da kamfe a sauran sassan kasar.
Yari ya bukaci hadin kan 'yan jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki a Zamfara domin samun nasarar tallata nasarorin gwamnatin Tinubu ga al'umma.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya kare matakan da Bola Tinubu ya dauka, ya ce sun zama dole ne a kasar.
Asali: Legit.ng
