Bayan Shekaru Fiye da 30, An Dauko Abin da Tinubu Ya Ce kan Kujerar Shugaban Kasa a 1992
- Babban lauya Wole Olanipekun (SAN) ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayyana burinsa na jagorantar Najeriya tun a shekarar 1992 lokacin yana sanata
- Ya ce Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da majalisar dokoki ta ƙasa a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida
- Tinubu ya halarci bikin cikar Olanipekun shekaru 75, shekaru 50 a aikin lauya da kuma shekaru 35 da zama babban lauya (SAN)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babban lauya a Najeriya, Wole Olanipekun (SAN) ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana burinsa na mulkin Najeriya tun a shekarar 1992, lokacin da yake sanata.
Olanipekun ya ce Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga majalisar dokoki ta ƙasa a lokacin ƙaddamar da ita ƙarƙashin gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Source: Facebook
Babban lauyan ya ce ya shaida wannan lamari ne a lokacin da yake matsayin Antoni-Janar na tsohuwar jihar Ondo, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da yake jawabi ranar Alhamis a wajen ƙaddamar da littafinsa mai suna Wole Olanipekun Through the Cases, a Abuja, ya ce kalaman Tinubu kan dimokuraɗiyya da burinsa na jagorantar ƙasar sun yi tasiri sosai a zuciyarsa.
Abin da Tinubu ya fada a 1992
A cewar Olanipekun, Tinubu, wanda yake jawabi a madadin sauran sanatocin da yake tare da su, ya gaya wa Babangida cewa suna da matuƙar sha’awar dorewar dimokuraɗiyya saboda wasu daga cikinsu suna fatan mulkar Najeriya a nan gaba.
Olanipekun ya ce:
“Ka gaya wa Shugaba Babangida cewa dukkanmu a wannan ƙasa, musamman ku sanatoci, muna tsananin goyon bayan dimokuraɗiyya, domin wata rana mutane irinku suna son mulkar wannan ƙasa. Wannan ya faru ne a 1992.
“Da ikon Allah, a shekarar 2023, ka zama shugaban Najeriya. Ga ka a nan a yau kana zaune a matsayin shugaban ƙasar Najeriya.
“Ba ka san hakan a wancan lokacin ba, amma kamar yadda aka ce, abin da ke cike a zuciya shi ne baki ke furtawa. Ka faɗi hakan, kuma ga shi ya tabbata.
Tinubu ya halarci kaddamar da littafin
An gudanar da bikin ƙaddamar da littattafan, waɗanda suka ƙunshi shari’o’in da kamfanin lauyoyinsa na Wole Olanipekun & Co. ya gudanar, a harabar Body of Benchers Complex da ke Abuja.

Source: Twitter
Bikin ya kuma kasance wani ɓangare na murnar cikar Olanipekun shekaru 75 da haihuwa, shekaru 50 da shiga aikin lauya a Najeriya da kuma shekaru 35 da samun matsayin babban lauya (SAN).
Tinubu ya halarci bikin, inda kaddamar da littattafan tare da karrama babban lauyan da lambar yabo ta Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).
Tinubu ya dauki darussa daga Buhari
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce ya koyi darussa masu muhimmanci daga marigayi Muhammadu Buhari, musamman kan shugabanci, kishin ƙasa da kyawawan halaye.
Shugaban ƙasar ya bayyana marigayi Buhari a matsayin mutum na musamman wanda ya karya tsarin siyasar da aka saba gani a Najeriya.
Asali: Legit.ng
