Ana Batun Tikitin Pantami, Takarar Jamilu Gwamna Ta Samu Tagomashi a Gombe
- Dujuman Pindiga ya bayyana goyon bayansa ga Dr Jamilu Ishiyaku Gwamna domin ya zama gwamnan Gombe a zaɓen 2027
- Ya yi alkawarin amfani da tsarin siyasarsa da albarkatunsa wajen tallafa wa burin Gwamna na maye gurbin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya
- Gwamna ya ce idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali kan lafiya, ilimi, noma, samar da ayyukan yi da haɗin kan al’ummar Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Alhaji Ahmed Bulama Hassan, Dujuman Pindiga, ya bayyana goyon bayansa ga Dr Jamilu Ishiyaku Gwamna, wanda ke neman zama gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.
Dujuman Pindiga, wanda ɗan kasuwa ne, mai taimakon jama’a kuma Manajan Darakta na Northern Star Medicals Ltd, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar nuna goyon baya da ya kai wa Jamilu Gwamna a gidansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027

Source: Facebook
Ya yi alkawarin tattara tsarin siyasarsa da kuma amfani da albarkatunsa wajen tallafa wa burin Jamilu Gwamna na maye gurbin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Dalilin da ya sa ya goyi bayan Jamilu Gwamna
Dujuman Pindiga ya ce ya yanke shawarar goyon bayan Jamilu Gwamna ne bayan duba irin halayensa na jagoranci, ƙwarewarsa, amincinsa da kuma yadda yake damuwa da jin daɗin jama’a.
Ya bayyana ɗan takarar a matsayin shugaba mai tawali’u da sauƙin kai, wanda ke da kyakkyawar alaƙa da al’ummar karkara da sauran jama’a.
“Na san Sardaunan Gombe tsawon shekaru da dama. Mutum ne mai tawali’u, mai tsoron Allah, mai sauƙin kai kuma wanda yake da kusanci sosai da talakawa."
“Kyautatawarsa ta shafi kowa ba tare da la’akari da bambancin matsayi ko ƙungiya ba,” in ji shi.
Ya ce Jamilu Gwamna zai faɗaɗa ci gaba
Dujuman Pindiga ya ƙara da cewa yana da yakinin Jamilu Gwamna zai iya ci gaba da ayyukan raya jihar da gwamnatin da ke kan mulki ta fara.

Kara karanta wannan
Pantami na murnar samun tikitin PDP, abokin hamayyarsa ya sha alwashin jawo masa matsala
Ya ce baya ga ci gaba da waɗannan tsare-tsare, Jamilu Gwamna zai iya faɗaɗa damammaki ga al’ummar jihar Gombe idan aka ba shi damar jagorantar jihar.
Gwamna ya bayyana abubuwan da zai sa a gaba
Da yake mayar da martani, Jamilu Gwamna ya gode wa Dujuman Pindiga bisa ziyararsa da kuma bayyana goyon bayansa ga takararsa.
Ya bayyana shi a matsayin ɗan jam’iyya mai kishin ci gaba da kuma mai tallafa wa harkokin matasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Jamilu Gwamna ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Gombe, gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga harkokin kiwon lafiya, ilimi, noma da samar da ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa zai kuma mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummar jihar Gombe.

Source: Facebook
Pantami ya aika sako ga 'yan APC
A wani labarin kima, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya sake dawo da maganar muhawara da ya nemi 'yan takarar gwamna su gabatar a jihar.
Sheikh Pantami ya yi zargin cewa wasu 'yan APC na yada farfaganda game da hukuncin da kotu ta yi a kan jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng