Da Sauran Rayuwa: Tsohon Sanata Mai Shekaru 70 Ya Ƙara Aure a Najeriya

Da Sauran Rayuwa: Tsohon Sanata Mai Shekaru 70 Ya Ƙara Aure a Najeriya

  • Tsohon Sanatan Kogi ta Gabas mai shekaru 70, ya auri sabuwar matarsa a wani bikin aure da aka gudanar a birnin Abuja
  • An gudanar da bikin auren ne ranar 19 ga Satumba 2026, inda wani bidiyo ya nuna tsohon sanatan da amaryarsa suna rawa yayin bikin
  • Tsohon sanatan lauya ne kuma ɗan siyasa daga Idah, Kogi, wanda ya wakilci Kogi ta Gabas a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 da 2015

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Duk da tarun shekarunsa a duniya, wani tsohon Sanatan Kogi ta Gabas ya kara kinkimo wata sabuwar amarya.

Majiyoyi suka ce Sanata Emmanuel Dangana Ocheja, mai shekaru 70, ya auri sabuwar matarsa a wani bikin aure da aka gudanar Abuja.

Tsohon sanata mai shekaru 70 ya ƙara aure a Kogi
Tsohon sanata Emmanuel Dangana Ocheja yayin bikin aurensa a Kogi. Hoto: Punch.
Source: Instagram

An gudanar da bikin auren ne ranar 19 ga Satumba 2026, inda wani bidiyo ya nuna Ocheja da amaryarsa suna rawa yayin bikin, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya rasu a Najeriya, majalisar tarayya ta karrama shi

Ocheja, lauya kuma ɗan siyasa daga Idah, ya wakilci Kogi ta Gabas a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 da 2015 karkashin jam’iyyar PDP.

Ya kasance cikin Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta bakwai, inda ya yi aiki a kwamitoci da dama, ciki har da tsaro da sojoji, kasafi, gas da shari’a.

An haifi Ocheja ranar 3 ga Afrilu 1956, kamar yadda bayanan tarihinsa suka nuna. Ya karanci shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello, sannan aka kira shi Bar a 1982.

Daga bisani, ya koma jam’iyyar APC kuma ya ci gaba da taka rawa a siyasar jihar Kogi. Hoton bikin aurensa ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta.

Ƙarin bayani na tafe....

Sanatan Kano ya angwance a Najeriya

A baya, mun ba ku labarin cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya angwance da amaryarsa Hindatu Adda’u Isah, jami’ar sojojin saman Najeriya.

An daura auren ne a fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umar, lamarin da ya jawo cece-kuce saboda ya zo a ba-za-ta.

Manyan mutanen da aka hango sun halarci daurin auren Kawu Sumaila sun hada da A.A. Rano da Kabiru Alhassan Rurum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.