An Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan 19 a Jihohin Arewa a Zaben 2027

An Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan 19 a Jihohin Arewa a Zaben 2027

  • Kungiyar Atiku Bagudu Grassroots Network for Tinubu 2027 ta marawa Bola Ahmed Tinubu baya domin wa’adin mulki na biyu
  • Kungiyar ta yi alkawarin tattara kuri’u miliyan 19 daga jihohin Arewa 19 domin tabbatar da Tinubu ya yi tazarce a 2027
  • An nada Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, a matsayin uban kungiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi, Nigeria - A yayin da babban zaben 2027 ke kara karatowa, kungiyar Atiku Bagudu Grassroots Network for Tinubu 2027 ta marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin wa’adin mulki na biyu.

Kungiyar siyasan ta bayyana kudirinta na tattara wa Shugaba Bola Tinubu da APC kuri’u miliyan 19 daga jihohin Arewa 19 a zaben 2027.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a cikin shigar Hausawa a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta kuma nada Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, a matsayin ubanta.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun masa raddi mai zafi

Ta yanke shawarar marawa Tinubu baya ne bayan wani taro da ta gudanar a Abuja, wanda wakilai daga jihohin Arewa 19 suka halarta.

Ana shin tarawa Tinubu kuri'u a Arewa

A taron, mambobin kungiyar sun duba manufofi da shirye-shiryen gwamnati tare da tattauna dabarun tattara goyon bayan jama’a a matakin kasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Shugaban kungiyar, Hon. Ali Oriri, ya ce kungiyar za ta gina tsayayyen tsari a matakin al’umma a fadin Arewa domin tattara goyon baya ga Tinubu da kuma cimma burinta na samun kuri’u miliyan 19.

Oriri ya ce goyon bayan kungiyar ya samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin kokarin gwamnatin na sake fasalin tattalin arziki, karfafa ababen more rayuwa da aiwatar da sauye-sauyen da aka tsara.

Kungiya ta goyi bayan manufofin Tinubu

Ya ce cire tallafin man fetur, sauye-sauyen harkokin musayar kudaden kasashen waje da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da haraji da ake gudanarwa a yanzu matakai ne masu wahala, amma wadanda suka zama dole.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi Alƙawarin warware matsalar da ta fi damun yan Najeriya kan INEC da tsarin zabe

Kungiyar ta kuma ambaci zuba jari da ake yi a hanyoyi, layin dogo, wutar lantarki, gidaje, noma da sauran fannoni a matsayin wasu daga cikin dalilan da suka sa take neman a sake zaben Tinubu.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Alhaji Atiku Bagudu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ta ce ci gaba da wadannan manufofi na da muhimmanci domin bai wa sauye-sauyen damar kammaluwa da kuma haifar da karin damar tattalin arziki da inganta yanayin rayuwar ’yan Najeriya.

Ta kuma yi nuni da kokarin gwamnatin na kara kudaden shiga da karfafa harkokin kudin gwamnati ta hanyar sauye-sauyen kasafin kudi da haraji.

Za a fadada tallata Tinubu

Oriri ya ce kungiyar za ta kai kamfen dinta zuwa cikin talakawa a fadin Arewa, inda za ta tuntubi sarakuna, shugabannin addini, matasa da shugabannin al’umma a matsayin wani bangare na dabarun tattara goyon bayan jama’a.

Ya bukaci mambobin kungiyar da ke jihohin Arewa 19 su karfafa tsarin kungiyoyinsu tare da fara tuntubar masu kada kuri’a a kai a kai gabanin zaben 2027.

Shin Tinubu na cikin koshin lafiya?

Kun ji cewa jigon jam'iyyara adawa ta PDP, Otunba Segun Sowunmi, ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan lafiyar Shugaba Bola Tinubu.

Sowunmi ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya kuma hankalinsa yana kwance, yana ami cewa Tinubu na karfin ci gaba da mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262