Siyasa Ta Dauki Zafi, Yan Daba Dauke da Bindigu Sun Bude wa Magoya Bayan PDP Wuta

Siyasa Ta Dauki Zafi, Yan Daba Dauke da Bindigu Sun Bude wa Magoya Bayan PDP Wuta

  • Mutane uku sun jikkata, an lalata motoci yayin da wasu miyagu suka kai hari wurin tarukan tuntuba na PDP a jihar Cross River
  • Dan takarar gwamnan PDPna jihar Cross River ya ce ’yan bindiga sun kai hari kan tawagar magoya bayan jam’iyyar
  • ’Yan sanda sun ce sun tura jami’ai wuraren da lamarin ya faru, kuma yanzu komai yana karkashin kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Jam’iyyar PDP a Jihar Cross River ta yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hare-haren bindiga kan tarukan da ta shirya a Ƙaramar Hukumar Calabar South.

Jam'iyyar adawan ta yi ikirarin cewa maharan sun jikkata mutane uku tare da lalata motoci da dama a wurin tarukan PDP.

Jam'iyyar PDP.
Tutar daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya, PDP Hoto: @OfficialPDP
Source: Twitter

Dan takarar gwamnan PDP, Sir Arthur Javis Archibong, ne ya tabbatar da haka ga manema labarai bayan hare-haren, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan ta'adda sun rutsa manoma 15, sun masu mummunan aiki babu daɗin gani

Mahara sun tarwatsa tarukan PDP

Ya ce tashin hankalin ya fara ne a fadar Mai Martaba Sarkin Calabar South, Etubom Nyong Edet Okon I, lokacin da wasu ’yan bindiga suka tarwatsa taron.

Dan siysar ya ce an garzaya da mutanen uku da suka jikkata zuwa asibiti domin ba su magani.

Javis-Archibong ya ce lamarin ya ƙara muni a African Club da ke kan titin Calabar, wurin da aka tsara gudanar da taro na biyu, inda aka lalata motocin magoya bayan PDP.

Ya kuma yi zargin cewa maharan sun bude wuta kan ayarin motocin jam’iyyar PDP tare da lalata motocin da magoya bayanta suka mallaka.

Ya bayyana cewa kusan magoya baya 3,000 ne suka halarci taron, yana mai cewa an sanar da ’yan sanda tun farko kuma jam’iyyar ta yi tsammanin za a samar da isasshen tsaro.

Maimakon mayar da martani, ya ce jam’iyyar PDP ta hana magoya bayanta ramuwar gayya, sannan ta karkatar da ayarin motocinta zuwa wurin Kwamishinan ’Yan Sanda domin neman kariya.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Dan takarar ya ce PDP za ta kai ƙorafi ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro kan lamarin.

Cross River.
Taswirar jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

PDP ta kwantar da hankulan mutane

A wata sanarwa ta daban, Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a jihar, Mike Ojisi, ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin “hare-hare masu tayar da hankali” kan tarukan tuntubar jama’a na jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankula tare da guje wa ramuwar gayya, tana mai jaddada cewa tuntubar jama’a ta siyasa bai kamata ta zama sanadin tashin hankali ba.

’Yan sanda sun tura jami’ai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Cross River ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta tura jami’ai zuwa wuraren da abin ya faru kuma yanzu lamarin yana karkashin kulawa.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Sunday Eitokpah, ya ce rundunar na sane da lamarin.

Kakakin yan sandan ya ce:

“Domin kare lafiyar jama’a, ana shawartar mazauna yankin su kwantar da hankula, su guji wuraren da abin ya shafa idan ya zama dole, sannan su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Kara karanta wannan

An kama shugaban ƙungiyar magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso

Yan daba sun tashi taron APC

Kun ji cewa wasu tsagerun yan daba sun farmaki wurin taron jam'iyyar APC a jihar Ondo, inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.

An kuma ruwaito cewa an banka wa wasu motoci wuta a lokacin rikicin, sai dai har yanzu ba a san musabbabin rikicin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262