Sarkin Musulmi Ya Hango Tangarda a Hanyar da Wasu ke Shiga Addinin Musulunci a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Hango Tangarda a Hanyar da Wasu ke Shiga Addinin Musulunci a Najeriya

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ba za a tilasta wa kowa shiga Musulunci ba
  • Ya bukaci Musulmi su mutunta hakkoki da ’yancin mabiyan sauran addinai, yana mai gargadi kan tilasta wa wani canza addini
  • Majalisar NSCIA ta kuma bukaci a bunkasa ilimin addini da na zamani tare da kara wakilcin Musulmi a harkokin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi nasiha kan masu shiga addinin Musulunci.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa babu wanda ya kamata a tilasta wa shiga Musulunci, yana mai kira ga Musulmi da su mutunta hakkoki da ’yancin mabiyan sauran addinai.

Sarkin Musulmi.
Mai alfarma sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Ya kamata a tilastawa mutane su musulunta?

Kara karanta wannan

Faɗa da hadimin gwamna ya jawo matsala, an 'hana' limami sallar Juma'a

A rahoton Vanguard, Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen babban taron NSCIA da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa shiga Musulunci dole ne ya kasance bisa zabin mutum da yardarsa.

"Ba mu da niyyar tilasta wa kowa shiga Musulunci. Amma mun ga yadda mutane da dama suke shiga Musulunci bisa ra'ayin kansu, saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce babu tilastawa a cikin addini.”

Matsayar Sarkin ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan rashin hakurin addini da tashe-tashen hankula tsakanin mabiyan addinai daban-daban a kasar nan.

Sultan ya yi nasiha ga Musulmin Najeriya

A cikin ‘yan makonnin nan, Sarkin ya kuma yi kira ga Kiristoci da Musulmi da su guji zagin juna, yana mai cewa mutunta juna na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya.

Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci mabiyan addinan biyu su rungumi hakuri da juna, yana mai cewa sai musulmi sun zama masu gaskiya sannan za su tsira daga zagi.

Sarkin ya ce kada Musulmi ko Kiristoci su dauki kansu a matsayin wadanda suka fi sauran girma, yana mai jaddada cewa kowa daidai yake a gaban Allah, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

NSCIA ta bukaci inganta Ilimi

A nasa bangaren, Babban Sakataren NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bukaci iyayen Musulmi su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun samu ilimin addinin Musulunci da na zamani.

Oloyede ya ce ya zama dole matasan wannan zamani su samu nau’ukan ilimin biyu domin su iya bayar da gudummawa yadda ya kamata ga ci gaban kasa.

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III lokacin da ya karbi bakuncin Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Twitter

Ya ce:

“Jihohin da suka fi fama da koma baya a fannin ilimi jihohin Musulmi ne. Dole matasan wannan zamani su kasance masu kwarewa a ilimin Musulunci da na zamani.”

Ya kuma yi kira da a kara wakilcin Musulmi a kafafen yada labarai da wuraren aiki, inda ya bukaci shugabannin Musulmi su tabbatar da cewa ana duba cancanta wajen ba da muhimman mukamai.

Sarkin Musulmi ya aika sako ga Tinubu

Kun ji cewa ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, ta bukaci gwamnatin Tinubu ta gaggauta kawo karshen zubar da jini a Najeriya.

JNI ta ce hare-hare, kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci na ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin fargaba da rashin tabbas

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262