'Zan ba ku Man Fetur Kyauta': Dan Takarar Gwamna a Gombe ga Al'ummar Jihar

'Zan ba ku Man Fetur Kyauta': Dan Takarar Gwamna a Gombe ga Al'ummar Jihar

  • Dan takarar gwamnan Gombe a ADC, Bala-Bello Tinka ya yi alkawarin samar da man fetur kyauta ga al'umma
  • Tinka ya kuma yi alkawarin kyakkyawar kulawar lafiya kyauta ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da tsofaffi sama da shekaru 70
  • Ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa manoma, ‘yan kwangilar cikin gida, tare da nemo mafita ta dindindin kan matsalar ƙarancin ruwa a Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Dan takarar gwamna a ADC, Bala-Bello Tinka ya yi alkawura da dama ga al'ummar jihar game da zaben 2027.

Bello Tinka ya yi alkawarin samar da man fetur kyauta ga masu babura da kekunan haya idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.

Dan takarar gwamna zai ba mutane man fetur kyauta a Gombe
Dan takarar gwamnan Gombe a ADC, Bala Bello Tinka. Hoto: Bala Bello Tinka.
Source: Facebook

Tinka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon cikin gida a Gombe, wadda wakilin jaridar PUNCH ya saurara ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun masa raddi mai zafi

2027: Alƙawuran da Bala Bello Tinka ya ɗauka

Ya ce shirin na daga cikin matakan rage radadin matsin tattalin arziƙin da cire tallafin man fetur ya haifar.

Ɗan takarar ADC ya kuma sanar da raba man fetur kyauta na kwana ɗaya ga masu babura da kekunan haya domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Ya ce masu cin gajiyar shirin za su samu man a gidajen mai da aka ware a Gombe daga ƙarfe 6 na safe zuwa ƙarfe 6 na yamma ranar 1 ga Oktoba 2026.

Ya ce:

“Ranar 1 ga Oktoba, daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, duk mai tuka Okada da Keke Napep ya je gidajen man da muka ware ya karɓi man fetur kyauta. Wannan ita ce ƙaramar gudummawarmu wajen yin bikin tare da ’yan Najeriya da rage musu wahala."

Ya bayyana cewa masu motocin haya na daga cikin mutanen da cire tallafin man fetur ya fi shafa, yana mai cewa tallafin na da nufin ba su damar gudanar da bikin ranar ’yancin kai ba tare da fuskantar nauyin kuɗin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Tinka ya ƙara da cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da man fetur kyauta a matsayin wani ɓangare na matakan tallafa wa masu babura da kekunan haya.

Dan takarar gwamna a Gombe ya yi wa al'umma alkawura
Taswirar jihar Gombe da APC ke mulki karkashin Gwamna Inuwa Yahaya. Hoto: Legit.
Source: Original

Sauran alkawura da Tinka ya yi

Baya ga tallafin man fetur, ɗan kasuwar da ya koma siyasa ya bayyana wasu tsare-tsare da ya ce za su kasance ginshiƙan gwamnatinsa idan ya zama gwamnan Gombe.

A fannin kiwon lafiya, Tinka ya yi alkawarin samar da magani kyauta ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mazauna jihar da suka haura shekaru 70.

Ya ce:

“Za mu samar da kiwon lafiya kyauta ga yaranmu ‘yan ƙasa da shekaru biyar da iyayenmu tsofaffi. Babu wani yaro da ya kamata ya mutu saboda iyayensa ba su iya biyan kuɗin asibiti ba, kuma babu tsoho da ya kamata a bar shi ya mutu."

A fannin noma kuwa, ɗan takarar ADC ya ce gwamnatinsa za ta sauya tsarin sayen takin zamani, ta hanyar samo shi daga ’yan kasuwar cikin gida maimakon saye kai tsaye daga masana’antun da ke ƙera shi.

“Idan muka saya daga ’yan kasuwar cikin gida, kuɗin zai zauna a Gombe, ya riƙa zagayawa tsakanin mutanenmu kuma ya bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida. Haka ake bunƙasa Gombe."

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

- In ji Tinka

Ya ce shirin zai ƙarfafa ’yan kasuwar kayan noma na cikin gida tare da samar da ayyukan yi a sassa daban-daban na harkar noma.

Tinka ya kuma yi alkawarin bai wa ’yan kwangilar ’yan asalin Gombe fifiko wajen aiwatar da ayyukan gwamnati, yana mai cewa za a gayyato na waje ne kawai idan babu ƙwararrun da suka dace a jihar.

Ya ƙara da cewa:

“Muna da ƙwararrun injiniyoyi, magina da ’yan kwangila a Gombe. Za mu ba su aiki domin ƙwararrunmu na cikin gida su bunƙasa. Za mu fita waje ne kawai idan hakan ya zama dole."

Jamilu Gwamna ya shawarci Pantami, Tinka

A baya, an ji cewa dan takarar gwamnan APC, Jamilu Isiyaku Gwamna ya ce dandalin sada zumunta hanyoyin sadarwa ne kawai, amma ba ya maida farin jininsu ya zama kuri'u a zabe.

Wannan ce hudubar da Ibrahim Shawai ya yi wa masu neman takarar gwamnan jihar Gombe a shekara mai zuwa.

Dan takarar daga APCwato Jamilu Gwamna zai kece raini da ‘yan takara kamar su Isa Ali Ibrahim Pantami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.