Hankalin Dangote Ya Tashi kan Maido Tallafin Mai, Atiku Ya Masa Bayani Dalla Dalla
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya goyi bayan gargaɗin matatar Dangote kan tilasta mata sayar da man fetur a farashin da ba zai jawo mata riba ba
- Atiku ya ce tsarin tallafin da ya gabatar zai rage kuɗin samar da man fetur a matatun mai na cikin Najeriya, ba tare da tilasta musu sayar da shi cikin asara ba
- Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da karkatar da ma’anar shawararsa, yana mai cewa tallafin da yake son dawo da shi zai shafi man da aka tace a Najeriya ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya goyi bayan gargaɗin Matatar Dangote kan batun tilasta wa matatun mai sayar da man fetur a farashin da zai jefa su cikin asara.
Atiku ya ce shawararsa ta samar da tallafin mai ba za ta tilasta wa matatun mai na cikin gida sayar da man fetur cikin asara ba.

Source: UGC
Atiku ya kare Matatar Dangote
Vanguard ta rahoto cewa a wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya zargi Shugaba Bola Tinubu da karkatar da damuwar da Matatar Dangote ta bayyana.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin na yin hakan ne domin ta ɓata tsarin tallafin samar da mai da ya gabatar.
Ya ce ba daidai ba ne a umarci matatar da ta zuba biliyoyin daloli wajen saka hannun jari sannan a tilasta mata sayar da man fetur a ƙasa da kuɗin samar da shi.
Tsarin tallafin mai na Atiku
Atiku ya ce akwai bambanci tsakanin tsarin tallafin da yake gabatarwa da irin tallafin da ake bayarwa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
Ya ce:
“Tallafin shigo da mai yana amfani da kuɗin gwamnati wajen tallafa wa man fetur da aka tace a ƙasashen waje aka kawo Najeriya.
"Tallafin samarwa kuma zai tallafa wa ɗanyen mai da ake tacewa a Najeriya domin matatunmu su samar da mai cikin sauƙi, sannan ’yan Najeriya su biya kudi kadan.”
Ya ce za a rage kuɗin ɗanyen man da ake bai wa matatun cikin gida da suka cancanta ta hanyar tsari mai gaskiya, iyakar tallafi da kuma tantancewa mai zaman kanta.
Ya ƙara da cewa:
“Akwai babban bambanci tsakanin taimaka wa mai samarwa ya rage kuɗin samarwa da tilasta masa sayarwa cikin asara. Gwamnatin Tinubu ta san wannan.”

Source: Facebook
INEC ta goyi bayan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Atiku Abubakar kan zargin gabatar da jabun takardun shugaba Bola Tinubu.
Hukumar ta ce ƙarar da Atiku ya shigar ta ƙunshi cin zarafin tsarin shari’a, tana mai cewa ba ta bayyana wani ingantaccen dalilin da zai sa kotu ta ci gaba da sauraron ta ba.
Hukumar INEC ta kuma ce Atiku ba shi da haƙƙin shigar da ƙarar, tana mai cewa batutuwan da aka gabatar sun shafi zato ne da muhawarar ilimi kawai.
Asali: Legit.ng

