An Yi Caraf an Cafke Dan Bindiga da Ya Shiga Kasuwa Sayar da Akuyar Sata

An Yi Caraf an Cafke Dan Bindiga da Ya Shiga Kasuwa Sayar da Akuyar Sata

  • An kama wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan bindiga ne da hannu a satar dabbobi a Gidan Madi, ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto
  • An kama wanda ake zargin ne a kasuwa dauke da akuya da mai ita ya tabbatar da cewa tana cikin dabbobin da aka sace daga garinsu
  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce wanda aka kama ya kuma taimaka wa jami'ai da bayanan da ka iya kai su ga sauran waɗanda ake zargi da hannu a satar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan bindiga da hannu a satar dabbobi a yankin Gidan Madi, ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

An kama wanda ake zargin ne a wata kasuwa, inda aka same shi dauke da wata akuya da daga bisani mai ita ya gane cewa tana cikin dabbobin da aka sace daga al'ummar yankin.

Gungun 'yan bindiga
Wasu 'yan bindiga masu kai hare-hare. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da kama mutumin a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis.

Yadda aka kama dan bindiga

Rufai ya ce wanda aka yi wa fashin ya gane akuyar tasa, sannan ya kuma gane wanda ake zargin a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka shiga cikin satar dabbobin.

Ya ce wanda ake zargin da wasu abokan aikinsa sun je Jurelku, wani ƙauye da ke Gidan Madi, a ranar 15 ga watan Satumba, inda ake zargin suka sace dabbobin mutumin.

Kakakin ƴan sandan ya ce:

“An kama wanda ake zargin a kasuwa dauke da wata akuya. Mai ita ya gane akuyar, sannan ya gane wanda ake zargin da abokan aikinsa da suka zo Jurelku, ɗaya daga cikin ƙauyukan Gidan Madi, inda suka kwashe masa dabbobinsa.”

Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ana binciken wanda aka kama

Rahoton Tribune ya nuna cewa Rufai ya ce wanda ake zargin yana hannun ƴan sanda kuma yana ba su cikakken bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kashe wani matashi mai shayi a jihar Adamawa

Ya kara da cewa bayanan da aka samu daga wanda aka kama sun taimaka wa jami'an bincike wajen gano inda za a iya samun sauran mutanen da ake zargin suna cikin ƙungiyar.

“Wanda ake zargin yana tsare kuma yana ba mu cikakken bayani,”

In ji Rufai.

An kashe 'yan ta'adda 16

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta'adda 16 a wani samame da suka kai wani sansanin ƴan ta'adda a yankin Boima na ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.

Hakan na zuwa ne yayin da Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta rasa sojoji uku a hare-haren ƴan ta'adda da suka faru a wuraren da sojoji suke a Bataliya ta 226 da ke Garkida da Bataliya ta 232 da ke Garaha.

Jami'in Yaɗa Labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce hare-haren da ayyukan sojojin sun faru ne tsakanin ranar 30 ga Satumba zuwa 1 ga Oktoba 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng