Abin Tusayi: 'Yan Ta'adda Sun Rutsa Manoma 15, Sun Masu Mummunan Aiki babu Dadin Gani
- Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wa manoma kwanton bauna tare da kashe 15 daga cikinsu a karamar hukumar Marte ta jihar Borno
- Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kuma yi garkuwa da wasu manoma uku yayin harin da ya faru a Jihar Borno
- Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai cewa kai hari kan fararen hula laifi ne na yaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Mayakan Boko Haram sun yi wa wasu manoma kwanton bauna tare da kashe 15 daga cikinsu, yayin da suka yi garkuwa da wasu uku a Karamar Hukumar Marte ta Jihar Borno.
Majiyoyin yankin sun ce mummunan lamarin ya faru ne a kauyukan Ala, Gumna da Musune da ke kusa da hedikwatar karamar hukumar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun kai harin a yammacin Laraba, amma ba a kammala aikin kwashe gawarwakin ba sai safiyar Alhamis.
Yan ta'addan sun kashe manoma 15
Da yake bayyana abin da ya biyo bayan harin, wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
"Da farko an gano gawarwaki biyar a gona, yayin da aka gano wasu daga baya. Har yanzu ba a san inda mutane uku suke ba, kuma majiyoyi sun ce mayakan sun yi garkuwa da su.”
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, DSP Kenneth Nahum Daso, ya tabbatar da cewa mutane 15 sun rasa rayukansu, yana mai cewa hukumomi na gudanar da bincike kan lamarin.
“Muna kokarin gano inda mutanen uku da har yanzu ba a san inda suke ba suke," innji shi.
Yadda mahara suka rutsa manoma
Wata ’yar uwan daya daga cikin wadanda aka kashe ta bayyana yadda aka aiwatar da kisan, tana mai cewa manoman sun je gonakinsu ne domin girbin amfanin gona lokacin da aka yi musu kwanton bauna.
A rahoton Punch, matar ta ce:
“An tilasta musu kwanciya a kasa sannan aka harbe su a kai daga kusa. Abin ya yi muni matuka, babu dadin gani."
A cewar matar, al’ummar yankin sun tattara karfinsu tare da shiga gonakin domin neman gawarwakin wadanda aka kashe, inda suka tabbatar da birne su bisa tsarin jana’izar Musulunci.
Amnesty ta yi Allah wadai da harin
Kisan ya jawo kakkausar suka, inda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin take hakkin dokokin jin kai na kasa da kasa.

Source: Original
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Juma’a, ta nuna matukar damuwa kan karuwar hare-haren da ake kai wa al’ummomin da ke cikin hadari a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta jaddada cewa kai hari da gangan kan fararen hula da kungiyoyin ta'addanci ke yi babban laifi ne na yaki.
Sojoji sun samu nasara a Borno
Kun ji cewa dakarun Operation Hadin Kai sun hallaka ’yan Boko Haram da ISWAP 1,106 tare da cafke sama da N300m na kuɗaɗen haram daga masu ɗaukar nauyinsu.
Sojojin sun cafke aƙalla mutane 758 da ke taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’addan wajen samar da kayan aiki da sauran buƙatunsu
Asali: Legit.ng

