Rikicin Aminu Ado da Sanusi II Ya Dawo Sabo a dalilin Hawa Doki a Kano
- Sansanin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya mayar da martani bayan Sarki Muhammadu Sanusi II ya hau doki a Kano duk da dokar da gwamnatin jihar ta sanya
- Sanusi II ya hau doki ne zuwa filin wasa na Sani Abacha domin halartar bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin Najeriya, inda aka ga magoya bayansa suna masa rakiya
- Sarkin Dawaki Babba kuma babban mamba a majalisar Aminu Bayero, Aminu Babba Dan’agundi, ya ce suna jiran ganin matakin da gwamnatin Kano za ta ɗauka kan abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Bangaren Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya mayar da martani bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya hau doki zuwa wani taro duk da dokar hana hawan doki da jerin gwanon Durbar da gwamnatin jihar ta sanya.
Sanusi II ya hau dokin ne ranar Alhamis zuwa filin wasa na Sani Abacha domin halartar bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin Najeriya, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran manyan baki suka halarta.

Source: Twitter
Martanin bangaren Aminu Ado
Daily Trust ta wallafa cewa Sarkin Dawaki Babba kuma babban mamba a majalisar Sarkin Bayero, Aminu Babba Dan’agundi, ya ce sansanin Bayero na jiran ganin yadda gwamnatin jihar za ta mayar da martani kan matakin Sanusi.
Dan’agundi ya ce magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero za su jira dawowar basaraken daga tafiyar da yake yi kafin su yanke shawarar matakin da za su ɗauka.
Ya ce idan dokar gwamnatin jihar ba ta shafi dukkanin sarakunan gargajiya ba, za su sanar da shirinsu na yin jerin gwanon hawan doki bayan tuntubar Sarkin na 15.
Za a yi hawan Yakasai
Dan’agundi ya ce idan aka shirya jerin gwanon, za a nufi Yakasai ne domin halartar bikin saukar karatun Alƙur’ani wanda dokar gwamnatin jihar ta shafa a baya.
Ya ce za a sanar da jama’a ranar da lokacin gudanar da jerin gwanon bayan dawowar Aminu Ado Bayero da kuma tuntubar majalisar masarautarsa.
Gwamnatin Kano ta sanar da takaita dukkan nau’o’in jerin gwanon Durbar da hawan doki a cikin birnin Kano tun ranar 27 ga Satumba har sai baba ta gani.
Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar Kano, bayan ta yi nazari kan yanayin tsaro da ya shafi ayyukan da aka shirya gudanarwa.

Source: Facebook
Sanusi ya magantu kan El-Rufa'i
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda ake yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Sanusi II ya kuma yi magana kan tsare tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa ya shafe wata bakwai a tsare ba tare da an yanke masa hukunci ba.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya tambayi ko yadda ake gudanar da wasu irin waɗannan shari’o’i ya shafi yaƙi da cin hanci ne ko kuma siyasa.
Asali: Legit.ng

