2027: Dawo da Tallafin Mai da Alkawura 6 da Atiku Ya Yi wa Talakawa

2027: Dawo da Tallafin Mai da Alkawura 6 da Atiku Ya Yi wa Talakawa

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi wasu muhimman alkawura gabanin zaɓen 2027, ciki har da dawo da tallafin man fetur
  • Atiku ya kuma yi alkawarin sake buɗe iyakokin ƙasa, magance matsalar tsaro cikin shekara guda, da kuma dawo da Nijar, Mali da Burkina Faso cikin ECOWAS
  • Haka kuma, ya yi alkawarin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa na Kudancin Najeriya da kuma sake duba tsarin rancen ɗalibai tare da yiwuwar yafe masu bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya gabatar da wasu manufofi da alkawura a farkon yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buɗe lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Ƙasa a ranar 19 ga Agusta, yayin da aka tsara gudanar da zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

Kara karanta wannan

INEC ta fadi abin da ake tsoro ya hana zaben 2027 zama sahihi

Atiku Abubakar a wajen taro
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O Ibe.
Source: Facebook

Tribune ta wallafa cewa Atiku, wanda ke neman zama shugaban ƙasa a karo na shida, ya yi alkawuran da suka shafi wasu muhimman manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

1. Dawo da tallafin man fetur

Ɗaya daga cikin manyan alkawuran Atiku shi ne dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar 19 ga Agustan 2026 yayin wata hira, inda ya ce bai ga isasshen bayani kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin ba.

Ya ƙara da cewa idan aka zaɓe shi, zai dawo da tallafin man fetur tare da tabbatar da cewa duk wanda ya saci kuɗin ya mayar da su.

2. Sake buɗe iyakokin ƙasa

Atiku ya kuma yi alkawarin sake buɗe iyakokin ƙasa na Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.

Ɗan takarar na ADC ya ce rufe ko takaita zirga-zirgar kan iyaka ya cutar da halastaccen kasuwancin ƙetare, tare da jefa wasu matasa cikin matsalar rashin sana’a.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Ya ce wasu al’ummomin Arewacin Najeriya sun dogara sosai da kasuwanci da ƙasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin.

3. Magance matsalar tsaro

Tsaro na daga cikin abubuwan da Atiku ya yi wa’adi mai girma a kansu, inda ya ce zai iya shawo kan matsalar tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaro a faɗin Najeriya cikin shekara guda.

Punc ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi abin da ya kira sakacin gwamnati da tsawaita matsalar rashin tsaro.

Atiku ya kwatanta yawan ‘yan sandan Najeriya da na Masar, yana mai cewa yawan al’ummar Najeriya na buƙatar ƙarin jami’an tsaro sosai.

Atiku Abubakar da abokin takararsa
Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi da suke takara tare a 2027. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

4. Dawo da kasashen ECOWAS

Atiku ya kuma gabatar da wani shiri na manufofin ƙasashen waje da ya shafi Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

Da yake magana da BBC Hausa, ya ce zai yi aiki domin ganin Nijar, Mali da Burkina Faso sun dawo cikin ƙungiyar ECOWAS idan aka zaɓe shi a 2027.

Ƙasashen uku sun fice daga ECOWAS bayan dakatar da su sakamakon juyin mulkin soja da aka yi a cikinsu, inda suka kafa ƙungiyarsu.

Kara karanta wannan

Shin da gaske Atiku zai sayar da bankin CBN idan ya zama shugaban kasa?

5. Bunƙasa tashoshin ruwa

Atiku ya kuma yi alkawarin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa da ke Kudancin Najeriya domin samar da daidaito wajen shigo da kaya da kuma jigilar su zuwa sassan ƙasar.

Ya ce bunƙasa tashoshin jiragen ruwa a Kudu da Kudu maso Gabas zai rage lokaci da kuɗin da ake kashewa wajen jigilar kayayyakin da aka shigo da su zuwa sauran sassan Najeriya.

Atiku ya ce a baya ya gana da kamfanonin safarar jiragen ruwa da masu bunƙasa jiragen ruwa a Turai domin tattauna yiwuwar bunƙasa tashoshin jiragen ruwa na Kudancin ƙasar.

Mutane na sayen fetur a gidan mai
Ana saka wa mai mota fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

6. Yafe bashin ɗalibai

Ɗan takarar ADC ya yi alkawarin sake duba tsarin bayar da bashin ga dalibai na NELFUND, tare da yiwuwar yafe bashin ilimi ga ɗaliban da suka cika sharuddan.

Vanguard ta wallafa cewa babban mataimakinsa na musamman kan sadarwa da Jama’a, Phrank Shaibu, ne ya bayyana matsayin Atiku a wata sanarwa.

A cewarsa, sake duba tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa ɗaliban Najeriya ba su kammala karatu cikin nauyin bashin ilimi ba.

Kara karanta wannan

2027: An samu matsala a taron hadakar jam'iyyun adawa domin kifar da Tinubu

Za a rage kudin man fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar IPMAN ta ce gidajen mai da ke Abuja za su fara rage farashin fetur a famfunansu cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Kakakin IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce dillalan na shirin daidaita farashinsu da dabarun sayar da kayayyaki da zarar sababbin kayayyakin man fetur sun fara shiga kasuwa.

Sai dai ya ce har yanzu ba a san takamaiman ranar da sababbin kayayyakin za su fara shigowa ba, yayin da ake sa ran sauye-sauyen za su kawo canji a kasuwar man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng