Wike ko Ribadu? Malami Ya Yi Hasashen Wanda Zai Zama Shugaban Ƙasa

Wike ko Ribadu? Malami Ya Yi Hasashen Wanda Zai Zama Shugaban Ƙasa

  • Fasto Ekong Ituen ya yi hasashen cewa wani na kusa da Shugaba Bola Tinubu zai iya zama mataimaki ko shugaban Najeriya
  • Ituen ya ce hasashen nasa ya samo asali ne daga abin da ya kira hangen nesa na ruhaniya, ba nazarin siyasa ba
  • Hasashen ya zo yayin da wasu na kusa da Tinubu kamar Nyesom Wike, Nuhu Ribadu da Godswill Akpabio ke tallafa wa shugaban a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani fitaccen malamin addini, Ekong Ituen, ya yi hasashen wani na kusa da Bola Tinubu zai iya zama shugaban ƙasa.

Ituen ya ce Nyesom Wike zai iya zama shugaban Najeriya ko mataimakinsa nan gaba a rayuwarsa bayan hasashen da ya gano.

An yi hasashen Wike zai zama shugaban ƙasa
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Lere Olayinka.
Source: Twitter

Ituen ya bayyana wannan hasashe ne a wani saƙonsa da ya wallafa a Facebook ranar Litinin, 28 ga Satumbar 2025.

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000

Hasashen fasto kan siyasar Wike

Malamin ya bayyana tsohon gwamnan Rivers a matsayin ƙwararren ɗan siyasa, tare da cewa yana da muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.

Ituen ya ce hasashen nasa ya samo asali ne daga abin da ya kira “hangen nesa na wahayi”, ba nazarin siyasa ba.

Ya kuma shawarci duk wani ɗan siyasa da ke samun sabani da Wike da ya nemi hanyar sulhu domin warware matsalolin tsakaninsu.

Ituen ya ce, bisa hangen nesansa na ruhaniya, ya ga Wike yana kan hanyar zama mataimakin shugaban ƙasa ko shugaban Najeriya.

Ya kuma yi kira ga Wike da ya mai da hankali kan lafiyarsa, sai dai bai bayyana takamaiman abin da ya sa ya bayar da wannan shawarar ba.

Hasashen Ituen ya zo ne a lokacin da Nyesom Wike ke taka muhimmiyar rawa wajen shirya yakin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

A ranar 25 ga Satumba, 2026, Wike ya bayyana cewa zai jagoranci tawagar yakin neman zaɓen Tinubu a Abuja da Rivers yayin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Fasto ya fadi kwarewar Wike a siyasar Najeriya
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: UGC

Babban burin Nyesom Wike a Najeriya

Tsohon gwamnan Rivers ya sha bayyana cewa babban burinsa a yanzu shi ne ganin Tinubu ya samu wa’adi na biyu.

Saboda haka, hasashen malamin ya bambanta da abin da Wike yake bayyana a bainar jama’a game da burinsa na siyasa.

Fasto Ekong Ituen ba sabon mutum ba ne wajen yin tsokaci ko hasashe kan manyan ‘yan siyasar Najeriya da al’amuran siyasar ƙasar.

Tun da farko, an ruwaito cewa Shugaba Tinubu na shirin ba Wike wani takamaiman matsayi wajen gudanar da yakin neman zaɓensa na 2027.

Majiyoyi sun ce ana iya bai wa tsohon gwamnan Rivers alhakin daidaita harkokin yakin neman zaɓe a Rivers da Abuja.

Abin da zai sa Wike murabus

A baya, an ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai saka shi ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya ce zai sanar da murabus dinsa ranar 17 ga Janairun 2027, idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers ba a zaɓen shugaban ƙasa.

Ministan ya bayyana cewa yana jagorantar haɗin gwiwar jam’iyyu a Abuja domin samun nasara, tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.