Jonathan Ya Tuna da Janar Abacha, Ya Fadi Abin Kirkin da Ya Yi Wa Mutanen Kabilarsa
- Goodluck Jonathan ya ce al’ummar Bayelsa za su ci gaba da nuna godiya ga marigayi Janar Sani Abacha saboda ƙirƙirar jihar a 1996
- Jonathan ya ce Bayelsa ta samu gagarumin ci gaba tun bayan ƙirƙirar jihar, duk da cewa har yanzu ba ta kai matsayin da ake fata ba
- Gwamna Douye Diri ya ce ƙirƙirar Bayelsa ta kuɓutar da al’ummar Ijaw daga abin da ya kira zalunci da rashin adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce jihar Bayelsa za ta ci gaba da nuna godiya ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha.
Goodluck Jonathan ya ce za su ci gaba da nuna godiya ga tsohon shugaban kasar ne saboda ƙirƙirar jihar a shekarar 1996.

Source: Facebook
Jonathan ya bayyana hakan ne a yayin bikin cika shekaru 30 da ƙirƙirar jihar Bayelsa da kuma bikin karramawa da aka gudanar a Yenagoa ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026 da daddare, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce ƙirƙirar Bayelsa daga tsohuwar jihar Rivers ta samar da wata jihar da galibin al’ummarta ’yan kabilar Ijaw ne.
Jonathan ya sadaukar da lambar yabo
A yayin bikin, Jonathan ya sadaukar da lambar yabon da aka ba shi ga marigayi Chief Diepreye Alamieyeseigha, wanda ya kasance shugabansa kuma jagoransa a siyasa.
Ya ce Alamieyeseigha ne ya fara shigar da shi harkokin siyasa ta hanyar naɗa shi a matsayin mataimakinsa lokacin da yake gwamnan jihar Bayelsa.
Jonathan ya kuma ce duk da yadda wasu matasa ke tambayar abin da jihar ke biki a kai bayan shekaru 30, Bayelsa ta samu gagarumin ci gaba tun bayan ƙirƙirarta.
“Bayelsa ta samu abubuwa da dama”
Jonathan ya ce har yanzu jihar ba ta kai matsayin da ya kamata ta kasance ba, amma yana farin ciki da irin ci gaban da aka samu.
“Ko da yake ba mu kai inda ya kamata mu kasance ba, ina farin ciki da inda muke. Ina farin ciki da an ƙirƙiri jihar Bayelsa, kuma mun samu abubuwa da dama."
“Mutane da yawa ba za su san hakan ba, amma mun samu gagarumin ci gaba tun bayan ƙirƙirar jihar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mutanen Bayelsa za su ci gaba da godiya ga marigayi Janar Sani Abacha, wanda ya sanya Bayelsa cikin jihohi shida na ƙarshe da ya ƙirƙira.
Gwamna Diri ya yabawa Abacha
Shi ma Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yabawa marigayi Janar Sani Abacha, yana mai bayyana godiya a madadin al’ummar Ijaw saboda ƙirƙirar jihar a ranar 1 ga Oktoba, 1996.
Diri ya ce Abacha ya cancanci a ci gaba da yabonsa saboda matakin da ya ɗauka na ƙirƙirar Bayelsa.
Ya ce hakan ya ba al’ummar Ijaw damar samun jihar da galibin mazaunanta ’yan kabilar Ijaw ne.
“Abacha ya kuɓutar da mu daga zalunci”
Gwamna Diri ya ce yana da muhimmanci ya riƙa ambaton sunan Abacha a jawabinsa saboda rawar da ya taka wajen ƙirƙirar Bayelsa.
Ya ce marigayi shugaban ƙasar na iya kasancewa da ma’anoni daban-daban ga mutane daban-daban, amma ga mutanen Bayelsa, Abacha shi ne mutumin da ya ce ya kuɓutar da su daga zalunci da rashin adalci.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
“Idan a kowane sashe na jawabina na ci gaba da ambatonsa, saboda abin da Allah ya yi amfani da shi wajen yi wa al’ummar Ijaw."
“Janar Abacha na iya nufin abubuwa daban-daban ga mutane daban-daban, amma ga mutanen Bayelsa, shi ne wanda ya kuɓutar da mu daga zalunci."
“Ya kuɓutar da mu daga rashin adalci kuma ya ba mu jihar da galibin al’ummarta ’yan Ijaw ne, bayan an rarraba mutanenmu zuwa jihohi daban-daban, lamarin da ya mayar da mu tsiraru a wasu daga cikinsu,” in ji Diri.

Source: Facebook
An ba Jonathan sarauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa masarautar Bauchi ta ba tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sarautar gargajiya na girma.
Masarautar ta ba Jonathan sarautar Jigon Bauchi saboda gudunmawarsa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Asali: Legit.ng

