'Ni na Ci Zaɓe a 2023': Kalaman Obi da Suka Dugunzuma Fadar Shugaban Ƙasa

'Ni na Ci Zaɓe a 2023': Kalaman Obi da Suka Dugunzuma Fadar Shugaban Ƙasa

  • Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi, ya tayar da ƙura bayan magana kan zaben shekarar 2023 da aka gudanar
  • APC ta ce Obi ya kamata ya shirya fuskantar wani rashin nasara a 2027, yayin da Abdulaziz Yari ya ce babu ɗan takarar da ya kai Tinubu
  • Obi ya ce zai iya kawo sauyi cikin shekaru huɗu, zai ci gaba da tsarin yawo da darajar naira, tare da mayar da hankali kan noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Jam’iyyar APC mai mulki ta kalubalanci ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, kan ikirarinsa cewa ya lashe zaben 2023.

Obi ya ce zai amince da sakamakon zaben 2027 ne kawai idan an gudanar da shi cikin gaskiya, adalci da sahihanci.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kinkimo maganar kisan Sardauna, ya bayar da shawara

Kalaman Obi sun fusata fadar shugaban kasa
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Mr Peter Obi, Bayo Onanuga.
Source: UGC

A wata hira da Arise News, Obi ya gabatar da tsarin mulki da nufin ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro

Ya kuma soki Shugaba Bola Tinubu kan yadda aka kashe Naira tiriliyan 16 da aka ce an samu daga cire tallafin man fetur.

Obi ya bayyana kashe kudaden gwamnatin Tinubu a matsayin abin ganganci, yana mai cewa bai dace da halin wahalar da ’yan Najeriya ke ciki ba.

Obi ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023 ne karkashin jam’iyyar Labour Party, LP, inda ya zo na uku bayan Tinubu da Atiku Abubakar.

Hakan ya kasance ne bisa sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana a hukumance.

Da aka tambaye shi game da zaben 2023, tsohon gwamnan Anambra ya dage cewa shi ne ya lashe zaben shugaban ƙasa.

Ya ce mutanen da suka gudanar da zaben sun san abin da ya faru da kuma dalilin da ya haifar da matsalar tattara sakamakon.

Kara karanta wannan

An cafke Hafsat kan zargin yaɗa rahoton cewa Opay za su bar Najeriya

Ya ce:

“Na lashe shi, kuma zan ci gaba da cewa matukar ina raye cewa na lashe zaben 2023. Wadanda suka gudanar da zaben sun san bayanan; sun san dalilin matsalar da abin da ya faru.”

APC ta ce Obi ya shirya fuskantar wani rashin nasara

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Abimbola Tooki, ya yi watsi da ikirarin Obi.

Ya ce babu yadda Obi zai iya lashe zaben shugaban kasa na 2023, domin INEC ba ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Ya ce:

“Ta yaya zai ce ya lashe zaben 2023? Ta yaya ya lashe shi? Ina sakamakon? Bai da wakilai a jihohin Arewa da dama. Me ya sa INEC ba ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba? Ya kamata ya shirya fuskantar wani rashin nasara da ke tafe a 2027.”

Dangane da tambayar Obi kan tasirin Naira tiriliyan 16 da aka ce an samu daga cire tallafin man fetur, Tooki ya ce ya kamata ya tambayi gwamnonin jihohi

Kara karanta wannan

'Neman fitina yake yi': Gwamnatin Benue ta yi martani mai zafi bayan jifan Peter Obi

Ya ce Obi ya kamata ya duba irin kudaden da gwamnatocin jihohi ke samu kafin zuwan Tinubu da kuma wadanda suke samu yanzu.

Tooki ya kara da cewa ya kamata Obi ya duba ko daliban manyan makarantu ba sa samun tallafin karatunsu daga NELFUND.

NDC ya samu nasara a kotu

An ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta amince da sabon tambarin NDC domin amfani da shi a zaɓe Kotun ta hana.

INEC dakatarwa ko tsoma baki wajen amfani da alamar nasara ta yatsu biyu da NDC ta ƙirƙira a matsayin tambarinta.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar NDC, bayan da jam’iyyar ta zargi INEC da cire sabon tambarinta tare da mayar da tsohon tambari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.