Gwamnatin Tinubu Za Ta Sanar da 'Yan Najeriya Kudin da Aka Samu daga Cire Tallafin Fetur
- Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fitar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗen waje
- Taiwo Oyedele ya ce tambayar da ‘yan Najeriya ke yi kan inda kuɗaɗen suka shiga tambaya ce mai inganci
- Ministan ya ce an yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen wajen biyan wasu basussuka da ƙarin kuɗin ruwa da kuma sabon mafi ƙarancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta fitar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka adana bayan cire tallafin man fetur da kuma abin da ta kira tallafin musayar kuɗaɗen waje.
Taiwo Oyedele ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026 yayin taron Africa Emerging Markets Forum karo na bakwai da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya

Source: Facebook
Oyedele ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayoyi kan ko ‘yan Najeriya suna ganin amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo, rahoton TheCable ya nuna hakan.
Ya amince cewa ‘yan Najeriya da dama suna tambayar abin da ya faru da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin, yana mai cewa damuwarsu ta dace.
Oyedele ya yi magana kan kuɗaɗen tallafi
“Ina kuɗin su ke? Na ji ana yawan yin wannan tambayar. Kuma kun san me? Tambaya ce mai inganci,” in ji shi.
A cewar Oyedele, gwamnati za ta fitar da cikakken bayani cikin ‘yan kwanaki kan adadin kuɗaɗen da aka samu da kuma yadda aka kashe su.
“Cikin ‘yan kwanaki, za ku ga cikakken bayani saboda mun yi imanin cewa wajibi ne a kanmu mu bayyana wa ‘yan Najeriya abin da muke yi. Wannan shi ne ma’anar gaskiya da bayyana komai a fili,” in ji ministan.
Ya ce haɗaɗɗen kuɗin tallafin man fetur da abin da ya kira “tallafin musayar kuɗaɗen waje” ya kai kusan kashi 5 cikin 100 na jimillar darajar tattalin arzikin Najeriya (GDP), jaridar Leadership ta kawo labarin.
Oyedele ya ce duk da cewa cire tallafin ya taimaka wajen ceto kuɗaɗen gwamnati, babban manufar matakin ita ce kawar da matsaloli da cin hanci da suka dabaibaye tsarin.
Inda aka yi amfani da kuɗaɗen
Oyedele ya ce an yi amfani da wani babban ɓangare na kuɗaɗen wajen cika wasu nauyin gwamnati da a baya ake ɗaukar nauyinsu ta hanyar kuɗaɗen da babban bankin ƙasa ke samarwa.
Ya ƙara da cewa an kuma yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan ƙarin kuɗin ruwa kan basussuka bayan tsaurara manufofin kuɗi da kuma aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Source: Twitter
A cewarsa, kafin aiwatar da sauye-sauyen, gwamnati na ɗaukar wani ɓangare na kuɗaɗenta ta hanyar ƙirƙirar kuɗi, yayin da kuɗin ruwa kan basussukan gwamnati suke ƙasa sosai.
“Idan kuka daina buga kuɗi, kashe kuɗin ba zai ɓace ba. Dole ne ku samar da kuɗin da kuke bugawa a baya. Wannan na daga cikin wuraren da kuɗaɗen da aka ceto suka shiga,” in ji shi.
Sakon Tinubu ga gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen gina hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Shugaba Tinubu ya bukaci gina hanyoyi ne maimakon gina gadar sama da ayyukan da ba su da amfani sosai ga jama'a.
Asali: Legit.ng

