Lauya Ya Tsage Gaskiya, An Ji Dalilin da Ya Sa Amurka ba Ta Kama Shugaba Tinubu ba

Lauya Ya Tsage Gaskiya, An Ji Dalilin da Ya Sa Amurka ba Ta Kama Shugaba Tinubu ba

  • Daya daga cikin lauyoyin Bola Tinubu ya ce rashin hujja kan zargin safarar miyagun kwayoyi ce ta hana Amurka kama shugaban kasa
  • Wole Afolabi ya ce kalubalantar da suka yi domin hana bude bayanan FBI da DEA ya yi daidai da hakkokin da dokar Amurka ta tanada
  • Lauyan ya ce babu wata takarda daga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da ta nuna ana boye bayanan domin kare Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani babban lauya a Najeriya (SAN) kuma mamba a tawagar lauyoyin Shugaba Bola Tinubu a Amurka, Wole Afolabi, ya yi karin haske kan zargin da ake wa shugaban kasa kan safarar miyagun kwayoyi.

Lauyan ya ce da a ce akwai hujjar da ke alakanta shugaban da safarar miyagun kwayoyi a Amurka, da hukumomin kasar sun kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai cigaba da aiki daga turai, babu zancen mika wa Kashim ragamar mulki

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da yake ganawa da wata tawaga a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Afolabi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Sunday Politics na Channels Television, inda yake amsa tambayoyi kan shari’ar da ake yi a halin yanzu game da fitar da rahoton FBI.

Yadda laiya ya nemi tono sirrin Tinubu

Bayanan dai su ne batun wata kara da wani lauya, Aaron Greenspan ya shigar, inda yake neman samun takardun da suka shafi Tinubu da binciken da aka gudanar kansa a baya.

Lauyan ya ce gwamnatin Amurka ta riga ta fitar da dubban shafuka na bayanan, amma tana son a bar wasu sassan a rufe, bisa hujjar cewa bayyana su na iya kawo cikas tare da tona asirin majiyoyi da jami’an da suka gudanar da binciken.

Dalilin neman hana sakin rahoton FBI

A cewar Afolabi, matakin da tawagar lauyoyin Tinubu ta dauka na kalubalantar fitar da sassan bayanan da aka rufe ya samo asali ne daga hakkokin da dokar Amurka ta bai wa kowa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kinkimo batun da yan Najeriya suka daɗe suna son sani game da Tinubu

“Wannan batu ya dade yana gudana, kamar yadda ka fada, kuma DEA da sauran hukumomin gwamnatim Amurka sun gabatar da takardu tare da bai wa Mista Greenspan.
“Yanzu Mista Greenspan yana neman a bude takardun da aka rufe kafin a mika masa su. Haka tsarin yake: ba abin da kake so ne ake dubawa ba, abin da doka ta tanada ake bi.
“Saboda haka, abin da muke yi shi ne yin amfani da kariyar da doka ta tanada. Hakkin da doka ta ba mu ne muke amfani da shi. Da ba mu yi amfani da abin da doka ta tanada ba, hakan zai zama gazawa a bangarenmu,” in ji shi.

Afolabi ya kuma yi watsi da ikirarin cewa gwamnatin Amurka na boye bayanan ne musamman domin kare Tinubu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bola Tinubu.
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dalilin Amurka na kin kama Tinubu

Afolabi ya ce hukumomin Amurka na daukar safarar miyagun kwayoyi a matsayin babban laifi, inda ya tambayi dalilin da zai sa Tinubu ya rika shiga Amurka ya kuma fita ba tare da an kama shi ko an gurfanar da shi ba.

Kara karanta wannan

'Matsala ne dawo da tallafin mai': Malamin Musulunci ya gargaɗi ƴan siyasa kan kamfe

Ya kawo misalan tsohon shugaban Panama, Manuel Noriega, da tsohon Firaminista Andrew Fahie, wadanda suka fuskanci gurfanarwa kan zarge-zargen da suka shafi miyagun kwayoyi.

“Saboda haka, tambayar da ya kamata a yi ita ce: Me ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kasance na daban har zai shigo Amurka ya fita daga Amurka ba tare da an kama shi, an tsare shi ko an yi masa tambayoyi kan wani abu ba?” in ji shi.

Afolabi ya ce rashin gurfanar da Tinubu a gaban kotu abu ne mai muhimmanci, yana mai jaddada cewa ka’idar ita ce mutum ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifinsa ita.

APC ta nemi a saki rahoton Tinubu

An ji cewa jam’iyyar APM ta bukaci hukumomin Amurka su bayyana sakamakon rahoton FBI kan zarge-zargen safarar miyagun kwayoyi danake wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

APM ta ce za a iya fitar da wasu sassan rahoton da ba za su jefa rayuka cikin hadari ko tona asirin shaidu da masu bincike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262