'An Yi Gangami domin Kayar da Tinubu,' Gwamnan APC Ya Yi Gargadi

'An Yi Gangami domin Kayar da Tinubu,' Gwamnan APC Ya Yi Gargadi

  • Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi zargin cewa mutanen da suka yi adawa da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a 2015 ne suke haɗa kai domin yaƙar Bola Tinubu a 2027
  • A wani bayani da ya yi a hira da manema labarai, Gwamna Okpebholo ya ce babu gurbi a Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai cewa bai kamata a sauya shugaban da ke kan mulki ba
  • Gwamnan ya kuma yi kira ga masu shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 da kada su ɓata kuɗinsu, yana mai cewa ‘yan siyasa za su karɓi kuɗin amma ba za su zaɓe su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Benin – Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi zargin cewa wasu daga cikin mutanen da suka yi yaƙi da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a zaɓen 2015 ne suke sake haɗa kai domin adawa da Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Okpebholo ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Benin zuwa Asaba, inda ya ce babu gurbi a Fadar Shugaban Ƙasa kuma bai kamata a sauya shugaban da ke aiki ba.

Gwamna Monday Okpebholo
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo. Hoto: Edo State Government
Source: Twitter

Maganar adawa da Tinubu

Daily Trust ta wallafa cewa Gwamnan Edo ya ce wasu daga cikin mutanen da ke son yin takara da Tinubu a 2027 sun taɓa riƙe wasu manyan mukamai a gwamnati.

Ya yi zargin cewa mutanen sun yi adawa da Jonathan a 2015 lokacin da tsohon shugaban ke ƙoƙarin samar da makarantu ga almajirai domin ba su ilimi da rage wasu matsalolin da ake fuskanta a yanzu.

A cewar Okpebholo, mutanen da suka yi adawa da Jonathan a lokacin sun sake haɗa kai domin hana Tinubu komawa kan mulki.

Ya ce babu gurbi a Aso Rock

Rahoton Punch ya nuna cewa Gwamna Okpebholo ya ce babu gurbi a Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai cewa ya kamata shugaba Bola Tinubu ya kammala shekara takwas.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnan, wanda bai bayyana sunayen mutanen da yake zargi da haɗa kai ba, ya kuma shawarce su da kada su ɓata kuɗinsu wajen neman takara.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fadi wanda zai iya nasara a 2027, ya cire Tinubu a lissafi

Wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya ce wasu ‘yan siyasa na iya karɓar kuɗin da ‘yan takara za su raba amma daga ƙarshe ba za su zaɓe su ba.

Maganar farashin man fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ce ‘yan Najeriya na samun saukin farashin man fetur da ake sayarwa a ƙasar idan aka kwatanta da wasu ƙasashe.

Okpebholo ya bayyana hakan yayin wani taron ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Benin zuwa Asaba, inda ya ce ya je Landan tare da abokinsa domin sanin farashin man fetur a can.

Ya ce bayan canza kuɗin zuwa Naira, litar man fetur a Ingila tana kai kusan N3,000, yana mai cewa farashin da ake sayar da man a Najeriya ya fi sauƙi idan aka kwatanta da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng