Atiku Ta Tayar wa Tinubu Hankali kan Kudirin Dawo da Tallafi Idan Ya Yi Nasara

Atiku Ta Tayar wa Tinubu Hankali kan Kudirin Dawo da Tallafi Idan Ya Yi Nasara

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta soki Atiku Abubakar kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓe a 2027
  • Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce shirin Atiku yaudara ne da zai iya kawo cikas ga tattalin arziki
  • Atiku ya ce bai taɓa adawa da cire tallafin ba, amma ya tambayi yadda aka kashe kuɗin da aka samu bayan cire tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani game da alwashin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya sha.

Fadar ta caccaki Atiku ne kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shekarar 2027.

Fadar shugaban kasa ta dura kan Atiku
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar jama’a, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaben 2027

Dawo da tallafi: Tinubu ya soki Atiku

Dare ya zargi Atiku da ƙoƙarin amfani da batun tallafin man fetur wajen yaudarar ’yan Najeriya domin samun nasarar siyasa a zaɓen 2027.

Ya ce matsayar Atiku na iya kawo cikas ga farfaɗowar da ake samu a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.

Dare ya ce:

“Atiku Abubakar, Furucinka na cewa za ka dawo da tallafin man fetur cike yake da munafunci da yaudara. Wannan hanya ce ta yaudarar jama’a domin jawo hankalin ’yan Najeriya da ba su san gaskiya ba su zaɓe ka.
“Farfaɗowar da ake samu a fannoni daban-daban na rayuwar ƙasarmu tana damunka, kuma za a dakatar da ita idan aka aiwatar da wannan tunani naka. Da yardar Allah, hakan ba zai faru ba, kuma duk mutanen kirki masu kishin ƙasa dole su tashi tsaye su yi adawa da kai.”
Atiku zai dawo da tallafin mai
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Alwashin Atiku kan dawo da tallafin mai

Atiku ya yi wannan alkawari ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da Legit Hausa ta bibiya, inda yake amsa tambayoyi kan cire tallafin man fetur da kuma yadda aka yi amfani da kuɗin da aka samu daga matakin.

Kara karanta wannan

Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da cikas, rikicin shugabanci ya raunana ta

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce tun farko bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma yana tambayar yadda aka kashe kuɗin da aka samu bayan cire shi.

Atiku ya ce:

“Tun farko ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba. Amma yanzu da aka cire shi, ina kuɗin? Ina aka kai kuɗin tallafin? Shin an yi amfani da su wajen inganta kiwon lafiya, ilimi ko tsaro?
“Idan na lashe zaɓen shugaban ƙasa, zan dawo da tallafin man fetur. Kuma duk wanda ya sace kuɗaɗen tallafin Najeriya dole ya mayar da su.”

Kudin da Tinubu ya tara bayan cire tallafin mai

A wani labarin, an ji cewa Ministan Kudi Taiwo Oyedele ya bayyana makudan kudi da gwamnatin Bola Tinubu ta samu dalilin cire tallafin man fetur.

Daga cikin kudin, gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da jihohi da ƙananan hukumomi suka raba Naira tiriliyan 10.4.

Oyedele ya ce gwamnati ta kuma samu karin kudaden shiga na Naira tiriliyan 3.1 tare da karbar bashin Naira tiriliyan 11.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.