Atiku Ya Yi Sabon Alkawari ga Ma'aikatan Najeriya, Ya Ce za Su Shana
- Dan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata
- Atiku ya ce albashin N70,000 ba shi da wata daraja saboda tsadar man fetur, abinci, sufuri da kudin haya da ake fama da ita a Najeriya
- Ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta fara aikin ƙara mafi ƙarancin albashi daga ranar farko da ta kama aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Atiku ya ce albashin N70,000 da ake biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ba shi da ƙima sakamakon tashin farashin man fetur, abinci, sufuri da kudin haya.

Kara karanta wannan
"Ka ba mutane hakuri," Atiku ya sake tono abin da Bola Tinubu ya aikata a Najeriya

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa Daraktan Sadarwa na Dabarun Gangamin Shugaban Ƙasa na ADC, Phrank Shaibu ya sanar ranar Lahadi, Atiku ya ce kara albashi na da muhimmanci sosai.
'N70,000 ta yi kadan'
Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin albashi mai yawa wanda zai yi daidai da halin tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu.
Ya ce a lokacin da aka ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 a watan Yulin 2024, an yi hakan ne bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago.
Ya kuma tunatar da cewa Tinubu ya ce za a sake duba albashin bayan shekaru uku, amma Atiku ya ce halin da ma’aikata ke ciki a yanzu ya nuna cewa N70,000 bai isa ya kare su daga tsadar rayuwa ba.
Magana kan farashin fetur
The Cable ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya ce idan litar man fetur ta kai N1,400, albashin N70,000 zai iya sayen lita 50 kacal.

Kara karanta wannan
Me ya yi zafi: An nemi wasu jiga jigan ADC an rasa a kwamitin yakin neman zaben Atiku
Ya tambayi abin da zai rage wa ma'aikaci bayan sayen man fetur, musamman wajen ciyar da iyalinsa, biyan haya da kuma samun kuɗin zuwa wurin aiki.
Atiku zai kara albashi
Atiku ya bukaci Tinubu ya bayyana matsayarsa kan ƙarin mafi ƙarancin albashi, yana mai cewa bai kamata a bar ma’aikata cikin doguwar tattaunawa ba tare da tabbataccen sakamako ba.
Ya ce idan aka zaɓe shi a 2027, zai fara aikin ƙara mafi ƙarancin albashi tun daga ranar farko da gwamnatinsa za ta kama aiki.
Ya kuma yi alkawarin ɗaukar matakan rage tsadar rayuwa, ciki har da tallafa wa samar da kayayyaki a cikin gida, shirye-shiryen tallafin jama’a da kuma wasu matakai a ɓangaren man fetur.

Source: Twitter
Ministan ya koka kan N70,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce mafi ƙarancin albashin N70,000 bai ƙara isa ya jure matsin tattalin arzikin da ma’aikata da sauran ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Keyamo ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron ƙasa na shekarar 2026 kan shirye-shiryen yin ritaya, inda ya yi kira da a gaggauta sake duba albashin ma’aikata domin ƙara musu ƙwarin gwiwar aiki.
Ya kuma ce ƙaruwar tsadar rayuwa ta rage darajar albashin N70,000, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago ke neman a sake duba mafi ƙarancin albashin ƙasa.
Asali: Legit.ng