"Ka Yi Yadda na Yi," Atiku Ya Sake Kinkimo Magana Mai Girma kan Bayanan Tinubu na Amurka
- Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu da ya bude bayanansa domin jama'a su bincika su
- Ya ce an binciki zarge-zargen da ake yi masa a zamanin gwamnatin Obasanjo amma babu kotun da ta same shi da laifi
- Atiku ya kalubalanci Tinubu ya bari a saki bayanan Amurka yan Najeriya su gani kmar yadda shi ya bari aka bincike shi a mulkin Obasanjo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya fitar da bayanansa domin jama'a su bincika su.
Atiku ya ce shi a shirye yake a binciki duk wasu bayanai da suka shafe shi, yana mai cewa sake yada tsofaffin zarge-zargen da ake yi masa wani yunkuri ne na karkatar da hankali daga zarge-zargen da ake wa Tinubu.

Source: Facebook
Dalilin dawo da batun zargin Atiku
Hakan na kunshe ne wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Juma'a, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce sake tayar da zarge-zargen da suka samo asali tun lokacin rikicin siyasa tsakaninsa da Olusegun Obasanjo alama da ke nuna Tinubu da yaransa sun rasa mafita.
Ya ce masu kare gwamnatin yanzu sun kasa kare matsalolin rayuwa da 'yan Najeriya ke fuskanta, saboda haka suka koma tono tsofaffin zarge-zarge domin karkatar da hankalin jama'a.
Atiku ya wanke kansa daga zargi
Atiku ya ce an riga an binciki zarge-zargen da ake yi masa ta hanyoyi daban-daban a lokacin rikicin siyasarsa da gwamnatin Obasanjo.
A cewarsa, hukumomin gwamnati da suka hada da EFCC, wani kwamitin bincike, Majalisar Dokoki ta Kasa da kotuna sun binciki batutuwan, amma babu wata kotu da ta same shi da laifi.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauko batun abin da ya faru da Tinubu a 1993, ya aika sako fadar shugaban kasa
Ya ce:
"Gwamnatin Obasanjo ba ta kare ni ba. A lokacin da rikicin siyasarmu ya yi kamari, an kai wadannan batutuwa gaban EFCC, wani kwamitin bincike, Majalisar Dokoki ta Kasa da kotuna.
"An yi amfani da dukkanin karfin gwamnati wajen binciken lamarin, kuma adawar siyasa a tsakanina da gwamnati a bayyane take. Duk da haka, babu wata kotu da ta same ni da laifi kan wadannan zarge-zarge."
Atiku ya ce duk wanda ke da sahihin hujja a kansa ya fito da ita domin a gwada ta a gaban doka.

Source: Twitter
Ya soki Tinubu kan batun bayanan FBI
Atiku ya kwatanta matsayarsa da na Shugaba Tinubu, inda ya yi nuni da shigar shugaban kasar cikin wata kara a Amurka da ke neman a saki wasu bayanan FBI da hukumar DEA da suka shafe shi.
Atiku ya ce kalubalensa a bayyane yake, wato a bude duk wasu bayanan da doka ta amince a bayyana sannan a gwada kowanne zargi bisa tsarin doka.
Ana neman EFCC ta binciki Atiku
Kun ji cewa Ehiozuwa Agbonayinma ya bukaci hukumar EFCC ta sake bude bincike kan wasu zarge-zargen almundahanar kudi da suka shafi Atiku Abubakar.
Lauyoyin tsohon dan Majalisar sun bai wa hukumar EFCC wa'adin kwanaki 14 ta dauki mataki kan bukatar ko kuma su maka ta a kotu.
Asali: Legit.ng

